Kotu ta bawa DSS umarnin ta kawo Dasuki gabanta kafin ta cigaba da shari'ar sa

Kotu ta bawa DSS umarnin ta kawo Dasuki gabanta kafin ta cigaba da shari'ar sa

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Maitama, Abuja, ta aike da takarda ga shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Yusif Magaji Bichi, a kan a gabatar da tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Sambo Dasuki, a kotu domin cigaba da shari'ar sa.

Alkalin kotun, Jastis Husseini Baba-Yusuf, ya bayar da umarnin ne a ranar Talata, biyo bayan rashin ganin fuskar Dasuki a kotu yayin cigaba da sauroron tuhumar sa da ake yi da cin amanar kasa da safarar kudi.

Ana tuhumar Dasuki tare da tsohon shugaban kamfanin dillancin man fetur na kasa (NNPC), Aminu Baba Kusa, da wasu kamfanoni guda biyu; Acacia Holdings Limited da Reliance Referral Hospital.

Ina Dasuki ya ke?, sai kun fito da shi - Kotu ta fada wa hukumar DSS

Sambo Dasuki
Source: UGC

Gwamnatin tarayya ta tsare Dasuki ne bisa zarginsa da yin amfani da ofishinsa wajen karkatar da makudan kudin da gwamnati ta ware domin sayen makamai ga rundunar sojoji da ke yaki da aiyukan ta'addanci da sunan kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

DUBA WANNA: Mai rabo ka samu: Hukumar kwastam ta bude sahafin daukan sabbin ma'aikata 3,200

Tun bayan kama shi a shekarar 2015, Dasuki na tsare a ofishin hukumar DSS duk da kotu ta sha bayar da umarnin a sake shi a kan beli, umarnin da gwamnatin tarayya tayi kunnen uwar shegu da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel