Wasu Samari da ke damfara sun burma hannun EFCC

Wasu Samari da ke damfara sun burma hannun EFCC

Dazu nan ne labari yake zuwa mana cewa wasu dubun wasu Matasa da su ka saba damfarar mutane babu gaira babu dalili ta hanyar yanar gizo sun shiga hannun jami’an hukumar EFCC a Najeriya.

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya ta kama wasu Bayin Allah matasa har 7 da ke amfani da zamba-cikin-aminci wajen satar dukiyar jama’a, ta hanyar yi masu karya da lambo.

Kamar yadda labari ya zo mana daga hannun hukumar EFCC da kan-ta, ta hannun jami’an ta, ana zargin wadannan Matasa da laifin zamba-cikin-aminci, da karya, da yaudara da lambo wajen samun makudan kudi daga Bayin Allah.

KU KARANTA: Kotu ta yankewa wasu Ma'aikatan N-power hukuncin dauri

Wasu Samari da ke damfara sun burma hannun EFCC

EFCC ta damke wasu masu damfarar jama’a ta yanar gizo
Source: Depositphotos

EFCC ta bayyana sunayen wadanda aka cafke a yankin Lekki da Ajah na cikin Garin Legas da; Abdulsalam Toheeb, Salam Sikiru, Abdusalam Rasaq, Azeez Oladimeji, Eniola Mogaji, Alabi Ridwan da kuma Asoroti Oluwaseun.

Daga cikin kayan da aka karbe a hannun wadannan Madamfara akwai manyan motoci kirar Honda Crosstour da Toyota Camry. Jami’an EFCC sun kuma samu na’urori irin su gafaka 7 da manyan wayoyin salula na zamani har 6.

EFCC ta shafin ta na Facebook ta tabbatar da cewa za a makawa wadannan samari a gaban kotu inda za a tuhume su da laifuffukan da aka ayyana domin ya zama darasi ga wasu masu wannan aiki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel