Dalilin mu na damke babbar alkaliya 'Ofili-Ajumogobia' a harabar kotu - EFCC

Dalilin mu na damke babbar alkaliya 'Ofili-Ajumogobia' a harabar kotu - EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta bayyana dalilinta na saka damke korarriyar alkaliyar babbar kotun tarayya, Jastis Rita Ofili-Ajumogobia.

A wani jawabi da shugaban sashen yada labarai da sadar wa, Tony Orilade, ya fitar a yau, Talata, EFCC ta ce ta sake kama Ofili-Ajumogobia ne domin samun damar sake shirya wasu sabbin tuhume-tuhume a kan ta.

Sanarwar ta kara da cewa, kama Ofili-Ajugomobia, ya biyo bayan wani hukunci da kotun daukaka kara a Legas karkashin Jastis Hyeladzira Nganjiwa ta taba yanke wa a kan cewar, ba za a iya gurfanar da alkali ko alkaliya ba har sai an kore shi daga aiki ko kuma hukumar kula da bangaren shari'a (NJC) tayi masa ritayar dole.

EFCC ta ce ta gurfanar da Jastis Ofili-Ajumogobia a gaban NJC kuma tunda sun dauki mataki a kan ta, yanzu zasu tunkari kotu da sabbin tuhume-tuhume a kan ta.

Dalilin mu na damke babbar alkaliya 'Ofili-Ajumogobia' a harabar kotu - EFCC

Jami'an EFCC da babbar alkaliya Ofili-Ajumogobia
Source: UGC

An fara gurfanar da Ofili-Ajumogobia da babban lauyan Najeriya (SAN), Godwin Obla, a ranar 30 ga watan Nuwamba na shekarar 2016 a kan wasu tuhume-tuhume 30 da suka hada da cin hanci, bayar da bayanan karya, tauye hukunci da sauransu.

Daga baya hukumar EFCC ta gyara tuhumar da ta ke yi masu daga guda 30 zuwa 31.

DUBA WANNAN: EFCC: Kotu ta yanke wa wasu 'yan N-power biyu hukuncin daurin shekara guda

Kafin fitar da jawabin na EFCC, Legit.ng ta sanar da ku cewar ana ta tafka takaddama a harabar babbar kotun Ikeja, yayin da jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) suka mamaye kotun domin cafke tsohuwar mai shari'ar a babbar kotun gwamnatin tarayya, Rita Ofili Ajumogobia.

Wannan kuwa ya biyo bayan watsi da karar da aka shigar ta laifuka 30 da EFCC ke tuhumar mai shari'a Ajumogibia da aikatawa, gaban mai shari'a Hakeem Oshodi. Ajumogibia na fuskantar tuhuma kan laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa da kuma amfani da ofishinta ta hanyar da ba ta dace ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel