Mun datse 'yan Boko Haram a gabar tafkin Chadi da dajin Sambisa - Buratai

Mun datse 'yan Boko Haram a gabar tafkin Chadi da dajin Sambisa - Buratai

A yayin da rundunar dakarun sojin Najeriya ke ci gaba da matsin lamba da kara kaimi wajen yakar ta'addancin kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram, kaifin ta'addancin kungiyar ya dakushe a yankin Arewa maso Gabas.

Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai

Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai
Source: Depositphotos

A ranar Litinin da ta gabata, shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ce tsanani na yaki da ta'addanci a yankin Arewa maso Gabas ya sanya kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ta turke kanta a dajin Sambisa da kuma gabar tafkin Chadi.

Babban sojin ya bayyana hakan yayin bayar da tabbacin sa ga al'ummar Najeriya na tsayuwar daka da jajircewa wajen gudanar da bincike domin gano ragowar 'Yan Matan Chibok da kungiyar Boko Haram ke ci gaba da garkuwa da su.

Buratai ya yi furucin hakan cikin jawaban sa kan gudanarwar rundunar soji a harkokin da suka shafi tsaro da yakar ta'addanci da ya gabatar a jami'ar Igbenedion da ke jihar Edo.

Shugaban hafsin sojin ya ce duba da tasirin jajircewa ta rundunar soji tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, ya sanya kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ke iya fuffuka kadai a cikin dajin sambisa da kuma gabar tafkin Chadi.

KARANTA KUMA: 'Yan siyasa ke da alhakin ta'addancin 'yan baranda da masu garkuwa da mutane - Falana

Ya kara da cewa, domin samun kyakkyawar makoma ta fuskar dimokuradiyya a Najeriya, akwai bukatar shimfida ingatattun tsare-tsaren tsaro da dabaru na siyasa wajen yakar ta'addanci makamancin na kungiyar Boko Haram.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel