PDP ta nemi INEC ta fito da kayan da aka aiki da su a zaben 2019

PDP ta nemi INEC ta fito da kayan da aka aiki da su a zaben 2019

Mun ji cewa Jam’iyyar hamayyar PDP a Najeriya tayi Allah-wadai da hukumar zabe mai zaman kan-ta na kasa watau INEC a game da kin bata kayan zabe da tayi kamar yadda kotu ta umarce ta da yi.

Kwanaki kotu ta bada umarni ga hukumar INEC ta fitowa PDP kayan da aka yi amfani da su wajen zabe domin ta gudanar da bincike amma hukumar kasar ta hau kujerar na-ki, ta ki cika wannan umarni na babban Kotun daukaka kara.

PDP ta bakin babban Sakataren ta na yada labarai na kasa baki daya, Kola Ologbondiyan, ta soki wannan mataki da INEC ta dauka inda jam’iyyar adawar ta kuma gargadi shugaban hukumar INEC na kasa Farfesa Mahmod Yakubu.

KU KARANTA: Kotu ta karbe kujerar wani 'Dan Majalisa bayan ya ci zabe

PDP ta nemi INEC ta fito da kayan da aka aiki da su a zaben 2019

Kakakin PDP yayi tir da INEc na kin bin umarnin Kotun Najeriya
Source: UGC

Kola Ologbondiyan yake cewa Mahmood Yakubu na INEC, yana iya jefa kasar cikin wani hali na ha’ula’i a dalilin tuburewa shari’ar da babban kotun daukaka kara tayi. PDP tana so INEC ta bata na’urorin aikin zaben da wasu fam.

A jawabin da Ologbondiyan ya fitar a madadin PDP, ya bayyana cewa INEC tana kokarin taka gaskiya da yi wa doka kememe da karon-tsaye. Babbar Jam’iyyar adawar tana sa rai gaskiya ta bayanna idan aka fito da kayan zaben.

Kakakin na PDP yake cewa kin sakin kayan zaben da aka yi amfani da su da INEC tayi, ya nuna cewa hukumar ta hada kai da manyan jam’iyyar APC wajen ganin an hana ‘dan takarar PDP, Atiku Abubakar, samun nasara a kotu

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel