Wata mata ta gurfana gaban kotu saboda ta doki yarinya mai shekara 9 da ice mai ci da wuta

Wata mata ta gurfana gaban kotu saboda ta doki yarinya mai shekara 9 da ice mai ci da wuta

-Wata mata ta zalunci wata yarinya ta hanyar dukanta da ice mai ci da wuta a baki

-Kotun majistiri dake sauraron wannan kara ta aminta da bada belin wannan matar akan kudi naira dubu hamsin

Matar yar shekara 34 mai suna, Oluwafunmilola ta bayyana a gaban kotun majistiri ta Ado-Ekiti bisa ga zarginta da ake na dukan yarinya yar shekara tara da ice mai ci da wuta a bakinta. Yan sanda ne sukayi awon gaba da wannan mata wacce ba suyi wata-wata ba sai suka makata kotu.

Yayinda yake shigar da wannan kara, Insfeto Caleb Leramo ya shaidawa kotun cewa wacce ake tuhuma ta aikata wannan laifin ranar 12 ga watan Afirilu a unguwar Ilupeju dake Ado-Ekiti. Yace yarinyar dai marainiyace kuma hakika wannan matar ta zalunceta.

Burning firewoods

Burning firewoods
Source: UGC

KU KARANTA:Dakatar da Onnoghen na da nasaba da siyasa

Bugu da kari, Leramo ya bayyana ma kotu cewa matar tayi amfani ne da ice mai ci da wuta inda ta doki yarinyar a baki hakan ne ma yayi sanadiyar ta kone a kirjinta. Wannan laifin da tayi hakika ya ci karo da sashe na 338 na ‘Criminal Code’, a cikin dokokin Ekiti, 2012.

Wanda ya shigar da karar ya nemi kotun da ta daga sauraren wannan kara domin ya samu damar kawo mata shaidun da zata gamsu dasu.

Wanda kuwa ke kare wacce ake kara, mai suna Chris Omokhafe ya roki kotun data bada belin wannan mata tare da cewa hakan ba zai sa matar ta gudu ba.

Mai shari’ar wannan kotu mai suna, Taiwo Ajibade ta amince da belin da aka nema da cewa wacce ake tuhuma zata biya naira dubu hamsin kuma ta dage sauraron wannan kara zuwa 6 ga watan Mayu inda za’a dawo a cigaba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel