El-Rufai ya kori ma'aikatan sa

El-Rufai ya kori ma'aikatan sa

- Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya bukaci dukkanin 'yan majalisar sa suyi murabus daga nan zuwa 30 ga wannan watan

- Sai dai gwamnan ya ware wasu mutane da ya ce za su iya cigaba da rike mukaman su

Yayin da yake kokarin fara zabar 'yan majalisar gwamnatin sa a karo na biyu, gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya umarci dukkan 'yan majalisarsa da su gabatar da wasikun murabus din su daga nan zuwa ranar 30 ga watan Afrilun wannan shekarar.

Gwamnan zai yi amfani da wani tsari don yanke shawarar wadanda zai sake zaba don tafiya da su a karo na biyu, sannan gwamnan ya bai wa ma'aikatar kudi ta jihar Kaduna isashen lokaci don daidaita duk wata harka ta kudi a jihar.

A umarnin da ya bayar, ya nu na cewa duk wata takardar murabus da za a gabatar sai an hada da takardar ajiye aiki, dauke da sa hannun wannan ma'aikaci, da kuma sunan ma'aikatar da ya yi aiki.

El-Rufai ya kori ma'aikatan sa

El-Rufai ya kori ma'aikatan sa
Source: Depositphotos

Sanarwar da kakakin gwamnan jihar ya fitar, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa El-Rufa'i ya yi godiya ga dukkanin ma'aikatan, ga irin gudunmawarsu da hidima ga jihar a lokacin gwamnatinsa ta farko.

Ya ce: "Yayin da ya ke kokarin zabar wadanda za su taimaka mishi a gwamnatinsa karo na biyu, gwamnan ya ce ya bukaci dukkanin 'yan majalisarsa da su gabatar da takardun ajiye aikinsu. Sannan gwamnan ya hada kwamiti wacce za ta lura da hakan karkashin jagorancin mataimakiyarshi Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe.

KU KARANTA: Sai na yi nazari kafin na karbi mukami a hannun shugaba Buhari - Dan takarar shugaban kasa

"Ana bukatar masu wadannan mukaman su bi umarnin gabatar da takardun nasu: dukkanin kwamishinonin jihar, sakatarorin jiha, masu bada shawara ta musamman, daraktoci, manajoji, da sauran shugabannin wasu ma'aikatu da dai sauransu.

"Wadanda dokar ba ta hau kansu ba sun hada da:

1. Hukumar harkokin kasuwanci

2. Hukumar shari'a ta jiha

3. Hukumar zabe ta jiha

4. Hukumar harkokin jama'a

5. Ma'aikatar ruwa ta jiha

Saboda wadansu gyare-gyare da aka yi a gwamnatin jihar, an bukaci wadanda suke rike da wadannan mukaman da suma su zauna a mukaman su:

1. Kwamishinan kudi

2. Akawun gwamnatin jiha

3. Mai ba da shawara ta musamman, a harkokin tsarin mulki

4. Manajan Darakta na kamfanin cigaban harkokin kasuwannin jihar Kaduna

5. Manajan Darakta na kamfanin kasuwanci da harkokin kudi na jihar Kaduna

Sannan kuma da duk wasu wadanda aka ba su mukami a watanni shida da suka gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel