Jirgin kasa ya take mutane biyu a Kano

Jirgin kasa ya take mutane biyu a Kano

- Wani jirgin kasa ya bi ta kan wasu mutane guda biyu a jihar Kano, inda ta ke a wurin suka ce ga garinku nan

- Hukumar 'yan sanda ta jihar Kano ita ce ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai kuma har yanzu ba a bayyana mutane biyun da suka rasa rayukan nasu ba

A yau Talatar nan ne hukumar 'yan sanda ta jihar Kano tabbatar da rasuwar wasu mutane biyu, wadanda suka mutu ta sanadiyar jirgin kasa da ya bi ta kansu, a cikin birnin Kano.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar DSP. Abdullahi Haruna, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

Jirgin kasa ya take mutane biyu a Kano

Jirgin kasa ya take mutane biyu a Kano
Source: Twitter

Jami'in ya ce a yau Talatar nan 16 ga watan Afrilu, da misalin karfe 8 na safe hukumar 'yan sandan ta karbi rahoton cewa an samu gawarwakin wasu mutane biyu da ba a tantance ko su waye ba, wadanda aka banbare su daga jikin karfen jirgin kasa, wadanda jirgin ya bi ta kansu a cikin karamar hukumar Nasarawa da ke cikin kwaryar jihar ta Kano.

KU KARANTA: Hukumomin tsaro sun binciko wata makarkashiya da Atiku ya ke hadawa Buhari

A cewarsa, lokacin da 'yan sandan suka ziyarci wurin, su gano cewa daya daga cikin mutanen jirgin ya raba shi biyu ne.

Ya ce yanzu haka an kwashe gawarwakin zuwa asibiti, wanda bai bayyana sunansa ba. Jami'in hulda da jama'an ya yi kira ga jama'a da su lura da yin harkoki a kusa da hanyar jirgin domin gujewa asarar rayuka a nan gaba.

Har yanzu dai ba tabbatar da mutane biyun da suka rasa ran nasu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel