EFCC: Kotu ta yanke wa wasu 'yan N-power biyu hukuncin daurin shekara guda

EFCC: Kotu ta yanke wa wasu 'yan N-power biyu hukuncin daurin shekara guda

Jastis I. M. Sani na babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a garin Fatakwal, jihar Ribas ya yanke wa Sata Owugha Clinton da Bolounmubofa Blessing Soroh hukuncin daurin shekara guda a gidan yari bayan samun su da aikata laifin sojan da sunan wani domin cin moriyar shirin gwamnatin tarayya na tallafa wa matasa marasa aiki, wato N-Power.

Ofishin hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) da ke Fatawal ne ya gurfanar da mutanen biyu bisa tuhuma guda daya; wato yin sojan gona. Laifin da ya saba wa sashe na 22(3) (a) na kundin laifukan aiyukan ta'addanci ta yanar gizo na shekarar 2015, wanda sashe na 22(4) ya tanadi hukuncinsa.

Clinton da Soroh sun shiga matsala ne bayan sun yi amfani da sunan Lovedy Chiamaka Uzor wajen shiga cikin masu cin moriyar shirin N-Power, wanda har ya kai ga sun karbi kudin da yawansu ya kai N360,000 a karkashin shirin.

Sun samu damar yin hakan ne bayan sun yi nasarar bude asusun banki da sunan Lovedy, wacce ta fara neman cin moriyar shirin na N-power amma ta ji tsoron ko akwai alamun cuwa-cuwa a cikin shirin.

EFCC: Kotu ta yanke wa wasu 'yan N-power biyu hukuncin daurin shekara guda

Jami'an EFCC
Source: Depositphotos

Masu laifin sun yi amfani da hakan tare da karasa cike neman cin moriyar shirin da sunan Lovedy.

Lovedy ta gano hakan ne bayan bankinta ya tabbatar ma ta da cewar tana daga cikin masu cin moriyar shirin N-power yayin da ta tuntube su.

DUBA WANNAN: Zamfara: Buhari zai kaddamar da sabbin jiragen yaki na musamman

Bayan kotun ta karanta musu tuhumar da ake yi musu, wadanda aka gurfanar din sun amsa laifin su.

Bayan sun amsa laifin nasu ne, sai lauyan mai kara, Alao Rashidat, ta roki kotun da ta yanke wa masu laifin hukunci bisa tanadin da dokar da ta haramta aikata laifuka ta yanar gizo.

Bayan rokon lauyan ne, sai alkalin kotun, Jastis Sani, ya yanke musu hukuncin daurin shekara duda a gidan yari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel