Ku fitar da shugabannin majalisa ko ku fadi zabe 2023 - Nabena ya gargadi jam'iyyar APC

Ku fitar da shugabannin majalisa ko ku fadi zabe 2023 - Nabena ya gargadi jam'iyyar APC

- An gargadi jam'iyyar APC ta fitar da shugabannin majalisar dattawa da ta wakilai, ko ta fadi zaben 2023

- An kuma bukaci jam'iyyar ta yi adalci wurin fitar da shugabannin a yankunan kasar nan

Mataimakin sakataren yada labarai na jam'iyyar APC na kasa, Yekini Nabena, ya gargadi jam'iyyar APC idan ba ta yi da gaske ba wurin zabar shugabannin majalisar dattijai, da kakakin majalisa, akwai yiwuwar jam'iyyar ta fadi zabe a shekarar 2023 sanadiyyar hakan.

Ku fitar da shugabannin majalisa ko ku fadi zabe 2023 - Nabena ya gargadi jam'iyyar APC

Ku fitar da shugabannin majalisa ko ku fadi zabe 2023 - Nabena ya gargadi jam'iyyar APC
Source: UGC

Nabena ya yi wannan gargadi ne a yau Talatar nan lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, ya yi kira ga shugabannin jam'iyyar APC da su tabbatar da sun tsaya sun tsara wadanda za su tsayar a matsayin shugaban majalisar dattijai, mataimakin shugaban majalisar dattijai, kakakin majalisa, da kuma mataimakin kakakin majalisa a wannan sabuwar gwamnatin, sannan kuma su tabbatar da aldalci a yankunan kasar nan, tunda shugaban kasa ya zo daga yankin arewa ta yamma, mataimakin shi ya fito daga yankin kudu ta yamma.

KU KARANTA: Hukumomin tsaro sun binciko wata makarkashiya da Atiku ya ke hadawa Buhari Nabena ya ce a yanzu haka shugabannin jam'iyyar APC karkashin Adams Oshiomhole, sun ba da kujerar shugaban majalisar dattijai ga yankin arewa maso gabas, yanzu ya rage saura kujeru uku suka rage.

Ya ce, "Jam'iyyar APC ta zabi shugabannin majalisa a dukkanin yankunan kasar nan. Sannan kuma, jam'iyyar APC daa fadar shugaban kasa su yi tunani da kyau kafin yanke hukunci akan wadanda za su ba wa kujerun a majalisar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel