Ma’aikata sun roki Buhari da ya sa hannu akan sabon karancin albashi

Ma’aikata sun roki Buhari da ya sa hannu akan sabon karancin albashi

-Ma'aikatan Abuja na fatan Buhari ya sanya hannu kan sabon mafi karancin albashi kafin 1 ga watan Mayu

-A taimaka a sanya mana hannu akan sabon karancin albashi, inji ma'aikatan gwamnati dake Abuja

Mai’aikatan babban birnin tarayya sun roki Shugaba Buhari da ya sanya hannu akan dokar sabon mafi karancin albashi da majilasar tarayya ta kawo mashi ranar 27 ga watan jiya.

Wasu daga cikin ma’aikatan da suka samu zantawa da manema labarai ranar Talata a Abuja sun nuna damuwarsu kwarai dangane da tsaikon sanya ma wannan doka hannu da ba ayi ba har yanzu, inda suke cewa hakan ya haifar da kagara kwarai daga bangaren ma’aikatan.

Shugaba Buhari

Shugaba Buhari
Source: Twitter

KU KARANTA:Dakatar da Onnoghen na da nasaba da siyasa

Daya daga cikin ma’aikatan mai suna Kema Nwokedi tace, aikin kwamintin da aka nada akan sabon karancin albashi zai kammalune daga wurin shugaban kasa. A don haka ta roki shugaban kasa da ya sanya hannu akan dokar da gamayyar yan majalisun suka aike mashi da ita domin basu damar rage kuncin tattalin arziki.

Nwokedi ta sake kira ga Buhari da ya sanya hannu akan dokar domin ya kasance tamkar tukwicin hutun ista ga ilahirin ma’aikatan Najeriya.

Shi kuwa wani ma’aikaci mai suna Abdullahi Sani, ya roki shugaban kasan da ya dubi kukan ma’aikatan ya taimaka ya sanya hannu kan dokar kafin ranar 1 ga watan Mayu.

Har ila yau wata ma’aikaciyar itama mai suna, Dayo Adebayo dake aiki a ma’aikatar kamfanoni da cinikayya ta kasa, cewa tayi idan aka sanyawa wannan doka hannu zata taimakama ma’aikatan kwarai da gaske.

Ta kara da cewa, tsaikon sanya hannun na haifar da matsanancin hali wurin ma’aikata duba ga cewa albashin da ake basu yanzu sam baya isa wajen biyan bukatunsu na yau da kullum.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel