Kalli adadin jam’iyyun siyasar da zasu gwabza a zabukan Ciyamomi da Kansiloli a Zamfara

Kalli adadin jam’iyyun siyasar da zasu gwabza a zabukan Ciyamomi da Kansiloli a Zamfara

Hukumar zabe mai zaman kanta na jahar Zamfara, ZASIEC ta sanar da adadin jam’iyyun siyasa guda Arba’in da uku (43) a matsayin iyakan jam’iyyun da zasu fafata a zaben shuwagabannin kananan hukumomi da za’a fafata a jahar.

Idan za’a tuna a ranar Litinin, 15 ga watan Afrilu Legit.ng ta ruwaito shugaban hukumar, Garba Muhammad ya sanar da ranar 27 ga watan Afrilun 2019 a matsayin ranar da zasu gudanar da zabukan kananan hukumomi a jahar gaba daya.

KU KARANTA: Najeriya na fitar da gangan mai miliyan 2.019 a duk rana ta Allah – Inji NNPC

Sai gashi an jiyo babban sakatare a hukumar ZASIEC, Bello Wadata yana bayyana adadin jam’iyyun da zasu shiga zaben yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Gusau, inda yace a yanzu haka sun fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki don su kammala shirye shirye.

“Mun samu ganawa da masu ruwa da tsaki, kuma zamu fara sayar musu da takardun cewa domin tsayawa takara nan bada jimawa ba, kuma ina baku tabbacin a shirye muke mu gudanar da zaben gaskiya da gaskiya a jahar Zamfara.” Inji shi.

Tun a ranar 2 ga watan Janairun 2019 ne wa’adin mulkin shuwagabannin kananan hukumomi dana Kansilolin jahar ya kare, amma majalisar dokokin jahar ta tsawaita musu wa’adin zuwa ranar 2 ga watan Mayun 2019.

Jahar Zamfara dai na fama da matsanancin matsalar tsaro da yaki ci yaki cinyewa, inda a yanzu haka ake kididdigan sama da mutane dubu uku, 3000, da rayukansu suka salwanta sakamakon hare haren yan bindiga.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel