Zargin taron dangi a Kaduna: Karya kake mana – hukumar INEC ga Shehu Sani

Zargin taron dangi a Kaduna: Karya kake mana – hukumar INEC ga Shehu Sani

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta mayar da martani ga Sanata Shehu Sani sakamakon zargin da Sanatan yayi na cewa wai INEC ta dauki hayar wani lauyan gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufai don ya wakilceta a gaban kotun sauraron korafin zabe na Kaduna.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Shehu Sani ya nuna kin amincewarsa da wannan lauya da INEC ta dauka don ya wakilceta a zaman kotun, inda ya danganta hakan ga wani bita da kulli da taron dangi da INEC da Gwamna El-Rufai ke shirin yi masa.

KU KARANTA: Abu naku maganin a kwabeku: Gwamna ya ware naira miliyan 13 don kiran waya

“Muna da tabbacin A.U Mustapha lauwan gwamnan jahar Kaduna Nasiru El-Rufai ne, don haka akan me INEC zata daukeshi ya zaman mata lauya a shari’ar da babu ruwan El-Rufai a ciki, don haka muke zargin El-Rufai da INEC na amfani da A.U Mustapha ne.” Inji shi.

Sai dai INEC ta bayyana ma Sanatan cewa tana daukan lauyoyi da dama aiki a rikice rikicen zabe daban daban da suka hada da na kafin zabe da kuma na bayan zabe, kuma lauyoyin nan sun bazu a sassan daban daban na Najeriya, don haka ba za ayi mamakin ko sun taba yi ma wasu aiki a baya ba.

Haka nan INEC ta cigaba da cewa tana bin kololuwar tsari wajen zaben lauyoyin da zasu kare muradunta, don haka babu yadda za’ayi ta hada kai da Gwamna El-Rufai wajen zaben lauyan da zai kareta a karar da Shehu Sani ya shigar da ita, tunda dai Gwamnan bai tsaya takarar Sanata ba.

Daga karshe hukumar INEC ta shawarci dukkanin bangarorin dake cikin shari’a dasu kwantar da hankulansu, kuma su amince da duk hukuncin da kotun za ta yanke domin kuwa tana da tabbacin kotun ba zata yi wata muna muna ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel