Buhari zai tsananta yaki da rashawa a wa'adi na biyu - Lai Mohammed

Buhari zai tsananta yaki da rashawa a wa'adi na biyu - Lai Mohammed

Ministan labarai da al'adu Alhaji Lai Mohammed, ya yi tuni tare da bayar da tabbacin sa akan yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai jajirce wajen kara tsanani a gwamnatin sa musamman ta fuskar yaki da cin da hanci da rashawa.

Alhaji Lai Mohammed

Alhaji Lai Mohammed
Source: Depositphotos

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Ministan labarai da al'adu Alhaji Lai Mohammed, ya bayar da shaidar cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tsananta yaki da rashawa a gwamnatin sa cikin wa'adi na biyu.

Alhaji Mohammed ya bayar da shaidar hakan ga daukaci al'ummar duniya yayin ganawa da kafar watsa labarai ta Voice of America (VOA) a birnin Washington DC na kasar Amurka. Ya ce shugaba Buhari ba zai sassauta ba wajen ci gaba da tsananta akidu da tsare-tsare na yaki da rashawa.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Ministan ya ziyarci birnin Washington DC domin ganawa da manema labarai na duniya da manufa ta bayar shaidar nasarori da kwazon gwamnatin shugaban kasa Buhari yayin riko da akalar jagoranci ta Najeriya.

KARANTA KUMA: Orji Kalu ne zabin mu a kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa - Kabilar Ibo

Ministan ya hikaito yadda akida da kuma tsarin asusun gwamnatin na bai daya da gwamnatin shugaban kasa Buhari ta kaddamar tare da tsarin bayar da tukwici mai girman gaske masu fallasar yiwa tattalin arziki ta'annati su ka taimaka wajen dawo da makudan dukiyar kasa.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki ta'annati a Najeriya ta ce mutumin da ya fallasa kudin da aka gano cikin wani gida a unguwar Ikoyi da ke jihar Legas ya zama attajiri.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel