Yanzunnan: Jami'an EFCC sun kasa sun tsare domin cafke mai shari'a Ajumogobia

Yanzunnan: Jami'an EFCC sun kasa sun tsare domin cafke mai shari'a Ajumogobia

Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa ana ta tafka takaddama a harabar babbar kotun Ikeja, yayin da jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC suka mamaye kotun domin cafke tsohuwar mai shari'ar babbar kotun gwamnatin tarayya, Rita Ofili Ajumogobia.

Wannan kuwa ya biyo bayan watsi da karar da aka shigar ta laifuka 30 da EFCC ke tuhumar mai shari'a Ajumogibia da aikatawa, gaban mai shari'a Hakeem Oshodi.

Ajumogibia na fuskantar tuhuma kan laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa da kuma amfani da ofishinta ta hanyar da ba ta dace ba.

Sai dai kotu na ganin wannan abu da EFCC ta yi a matsayin batawa shari'a lokaci.

KARANTA WANNAN: Labari mai dadi: Yadda injiniyoyi 2,000 za su samu aiki a matatar man Dangote

Yanzunnan: Jami'an EFCC sun mamaye kotu domin cafke mai shari'a Ajumogobia

Yanzunnan: Jami'an EFCC sun mamaye kotu domin cafke mai shari'a Ajumogobia
Source: Depositphotos

Mai shari'ar ya yi watsi da karar EFCC akan cewar ya soke karar ne saboda an daukaka karar shari'ar a madadin wani mai shari'ar da ake zargi da cin hanci da sharawa.

Oshodi ya zargi EFCC da batawa kotun lokaci a yayin da ta ke ci gaba da gabatar da shaidu.

Ajumogobia wacce ke sanye da kafar roba a kafar ta ta dama, ta yi yunkurin fita daga cikin kotun amma ta koma ciki bayan arangama da jami'an hukumar EFFC da ke dakonta domin su cafke ta.

A halin yanzu dai an boye mai shari'ar a hawan kotun na biyu, yayin da jami'an hukumar ke ci gaba da dakonta domin cafke ta.

Cikakken labarin yana zuwa...

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel