Wata kungiya ta bukaci Atiku ya fito ya baiwa al'ummar Najeriya hakuri

Wata kungiya ta bukaci Atiku ya fito ya baiwa al'ummar Najeriya hakuri

- Wata kungiyar hadin guiwa ta bukaci Atiku Abubakar ya tattare nashi ya nashi ya koma kasar shi ta asali da zama

- Sannan kungiyar ta bukaci Atikun ya fito ya bai wa 'yan Najeriya hakuri, sannan ya nemi takardun zama dan kasa kafin lokaci ya kure mishi

Wata kungiyar hadin guiwa a Najeriya ta yi kira ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, da ya fito ya bai wa al'ummar Najeriya hakuri sannan kuma ya koma kasar Kamaru ko kuma ya nemi Najeriya ta bashi katin zama dan kasa.

Kungiyar ta yi wannan kira ne bayan sanarwar da jam'iyyar APC ta fitar na cewa Atiku Abubakar ba dan Najeriya bane dan kasar Kamaru ne.

Wata kungiya ta bukaci Atiku ya fito ya baiwa al'ummar Najeriya hakuri

Wata kungiya ta bukaci Atiku ya fito ya baiwa al'ummar Najeriya hakuri
Source: Facebook

Kungiyar ta ce abinda Atiku Abubakar ya yi laifi ne babba, saboda haka ya fito ya bai wa 'yan Najeriya hakuri akan laifin da ya aikata.

A lokacin da ya ke magana da manema labarai, ranar Litinin din nan, Abdulmuminu Hassan, sakatare janar na kungiyar, ya ce tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida, ya ki ya bawa Atiku matsayin shugaban kwastan na Najeriya bayan ya gano cewa Atiku ba dan Najeriya ba ne.

KU KARANTA: Hukumomin tsaro sun binciko wata makarkashiya da Atiku ya ke hadawa Buhari

Hassan ya ce ya bawa Atiku Abubakar kwana 21 ya tattare kayan shi ya koma kasar Kamaru da zama.

Sannan mu na ba wa Atiku Abubakar shawarar ya fito ya bawa al'ummar Najeriya hakuri, ko kuma ya fito ya nemi takardar zama dan cikakken Najeriya. Ta wannan hanyar ce kawai 'yan Najeriya za su yafe mishi, tunda ya riga ya ta so a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel