Wata kungiya da ke goyon bayan Bago ta karyata tsayar da Gbajabiamila a matsayin Kakakin majalisa

Wata kungiya da ke goyon bayan Bago ta karyata tsayar da Gbajabiamila a matsayin Kakakin majalisa

- Wata kungiya ta bukaci jam'iyyar APC ta yi adalci wurin tsayar da Kakakin majalisar wakilai

- Kungiyar kuma ta karyata sanarwar tsayar da Hon. Femi Gbajabiamila a matsayin Kakakin majalisar wakilai

A kokarin da 'yan majalisar wakilai suke na hawa kujerar Kakakin majalisa, wata kungiya da take goyon bayan Hon. Mohammed Bago, ta yi watsi da bukatar jam'iyyar APC na tsayar da Hon. Femi Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisar wakilan, inda suka bayyana hakan a mastayin wata hanya da jam'iyyar ta bi domin kawo hatsaniya a cikin jam'iyyar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar ya fitar, Hon. Victor Afam Ogene a jiya, kungiyar ta ce ita a iya sanin ta jam'iyyar APC ba ta bayyana sunan kowa ba a matsayin wanda ta tsayar ya zama Kakakin majalisar, kawai dai ta bayyana cewar za ta tsayar da shugaban majalisar dattijai a yankin arewa maso gabas.

Wata kungiya da ke goyon bayan Bago ta karyata tsayar da Gbajabiamila a matsayin Kakakin majalisa

Wata kungiya da ke goyon bayan Bago ta karyata tsayar da Gbajabiamila a matsayin Kakakin majalisa
Source: Twitter

Ogene, tsohon dan majalisar wakilai, ya tabbatar da cewa, ko dan tabbatar da adalci da hadin kan jam'iyya kamata ya yi a tsayar da Kakakin majalisar a yankin arewa ta tsakiya.

Ya kara da cewa, Hon. Umar Mohammed Bago, ya na daya daga cikin wanda suka yi wa jam'iyyar APC hidima, saboda haka ya na fatan jam'iyyar APC za ta tsayar da shi a matsayin zabin ta na kujerar Kakakin majalisar wakilai.

KU KARANTA: Hukumomin tsaro sun binciko wata makarkashiya da Atiku ya ke hadawa Buhari

"Mun yadda da cewar jam'iyyar APC za ta yiwa al'ummar kasa da 'yan jam'iyya adalci ta ba wa dan arewa ta tsakiya kujerar Kakakin majalisar. Saboda ba zai yiwu a bai wa dan yankin da suke da mataimakin shugaban kasa ba, da kuma wasu manyan jigo a wannan gwamnatin.

"Saboda haka muna jira jam'iyya ta yi adalci, wanda shine ta tsayar da Bago a matsayin zabin ta na Kakakin majalisa," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel