Malaman addini sun bukaci Buhari da ya kara kaimi wajen hada kan yan Najeriya

Malaman addini sun bukaci Buhari da ya kara kaimi wajen hada kan yan Najeriya

Wasu malaman addini a jihar Lagas, sun bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi amfani da tazarcensa wajen kara kaimi ta bangaren inganta tsaro a Najeriya, hada kan al’umman kasar da kuma yin amfani da al’barkatun kasar waje sakeinganta kasar.

Malaman sun bayar da wannan shawarar ne a ranar Talata, 16 ga watan Afrilu a wata hira da kamfanin dillancin labaran ajeriya (NAN) a jihar Lagas.

Babban fasto na cocin katolika da ke Lagas, Most Rev. Adewale Martins, ya bukaci Shugaban kasar da ya kara kokari a fannin kare rayuka da dukiyar al’umman kasar.

Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya reshen jihar Lagas, Apostle Alexander Bamgbola, ma ya bukaci Buhari da yayi kokari wajen amfani da albarkatun kasar wurin ci gaban kasar.

Malaman addini sun bukaci Buhari da ya kara kaimi wajen hada kan yan Najeriya

Malaman addini sun bukaci Buhari da ya kara kaimi wajen hada kan yan Najeriya
Source: Facebook

Shugaban Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN), Fasto Olusola Ore, ya bayyana cewa ya kamata a duba lamarin cin hanci da rashawa da gaskiya ba tare da son kai ba.

KU KARANTA KUMA: Mun tsare Najeriya daga Boko Haram – Ministan labarai

Rev. Fr. Stephen Akinsowon, babban faston cocin Our Lady of the Holy Rosary, Ikeja yace: “Ina ganin sugaban kasar na bukatar kara kokari wajen hada kan yan Najeriya fiye da baya.

“Zan iya cewa ya amfana sosai daga kyawawan nufin yan Najeriya a mulkinsa na farko, amma a bayyane yake an kai ruwa rana kafin a shawo kan yan Najeriya su sake zabarsa a karo na biyu.

“Ina ganin ya kamata ya fara tunanin barin tarihi mai kyau ga yan Najeriya domin sunansa na alkhairi kada ya goge a zukatan al’umman kasar,” inji Akinsowon.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel