Yanda aka farmana tare da kashe yan uwanmu, inji wasu jama’ar Nasarawa

Yanda aka farmana tare da kashe yan uwanmu, inji wasu jama’ar Nasarawa

-Kimanin mutane goma sha biyar ne suka rasu sakamakon wannan harin, inji Gonji Thomas

- Daga ciki akwai wasu yan mata hudu yan uwa daya

Wata mata wacce ke zaune a Numan-chuko dake karamar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa, mai suna Maiwuya Bahago ranar Litinin ta bayyana mana yanda ta rasa 'yayanta mata guda hudu sakamakon harin da aka kawo masu wanda ake zargin cewa makiyaya ne.

Matar tace harin ya faru ne ranar Lahadi yayinda 'yayan nata suka halarci bikin zanen suna a makwabtansu. A cewarta wadansu mutane da ake zargin makiyayane sun sauka wannan wuri inda suka buda wuta da harbe-harben kan mai uwa da wabi.

makiyaya

makiyaya
Source: UGC

KU KARANTA:Buhari ya nemi goyon bayan kasashen dake makwabtaka da Najeriya wajen kare yaduwar makamai

Ta kara da cewa, “'Yayana hudu aka kashe jiya. Daya daga cikinsu ma tana dauke da juna biyu, daya kuma yaranta uku amma sauran guda biyun kuma basu da aure. Sun zo bikin zanen sunane inda a nan kuma suka hadu da ajalinsu.”

Matar tana rokon jama’a da su taimakamata yanda zata samu damar daukan nauyin marayun yaran da diyanta suka bar mata. “Bani da kowa wanda zai taimkameni saboda haka nake neman addu’a da kuma taimakon yan uwana yan Najeriya.”

A wata gabar kuwa, inda wadanda suka samu rauni ke karbar kulawa a babban asibitin Akwanga kamar yanda wani ma’aikacin asibitin ya bayyana mana. Akwai wani matashi mai suna, Maikasuwa Ngila wanda ya samu rauni a kafa, ya shaida mana cewa an harbeshi ne a kafa yayinda yake kokari guduwa daga wurin da aka kawo wannan hari.

“Na je bikin zanen suna ne jiya da yamma, kwatsam sai ga wasu mutane sun farma mana kafin kace kwabo suka fara harbe-harben kan mai uwa da wabi, a dai dai lokacinda muke kokarin guduwa ne suka harbe ni a kafa. Na gansu da idona makiyayane suka kawo harin.”

Da yake karin haske akan lamarin shugaban babban asibitin Akwanga, Gonji Thomas ya shaidawa yan jarida cewa mutum goma sha biyar dai an kawo su ne a mace yayinda wasu kalilan kuwa sun samu raunuka.

Mukaddashin kwamishinan yan sanda na jihar Nasarawa, Inusa Mohammed yace “a nasu bangaren suna nan suna gudanar da bincike domin samun duk wani bayanin da zai taimakesu wurin kama wadanda suka aikata wannan ta’addanci.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel