Mutum 55 sun raba N1.3bn a lokacin gwamnatin Jonathan – Ministan Buhari

Mutum 55 sun raba N1.3bn a lokacin gwamnatin Jonathan – Ministan Buhari

Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gano cewa yan Najeriya 55 ne suka yi rabon naira biliyan 1.3 a mulkin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Jimlan, a cewar shi, yayi dai-dai da adadin kudi da gwamnati mai ci ta kashe akan kayayyakin more rayuwa da cigaba a shekaru hudu.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa Mohammed ya bayyana hakan ne a Washington D.C a lokacin wata hira tare da muryar Amurka.

Mutum 55 sun raba N1.3bn a lokacin gwamnatin Jonathan – Ministan Buhari

Mutum 55 sun raba N1.3bn a lokacin gwamnatin Jonathan – Ministan Buhari
Source: Depositphotos

Sai dai bai bayyana sunan kowa ba amman ya sha alwashin cewa Buhari zai tabbatar da ganin an kwato duk kudaden da aka tsoffin gwamnati suka sata.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Alhaji Lai Mohammed yace gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi kokari sosai wajen magance matsalar rashin tsaro sannan ta tsare kasar fiye da yadda take a 2015.

KU KARANTA KUMA: Atiku dan Najeriya ne – Inji Yakasai

Musamman, yace gwamnatin ta yi nasarar kare gaba daya kasar daga hannun yan ta’addan Boko Haram yayinda aka kaw karshen rikicin makiyaya da manoma a Benue.

Mohammed ya bayyana cewa an sassaita yaki da ta’addanci, kasha-kashe da kuma fashi da makami a Zamfara da Kadua cikin makonni biyu da suka gabata saboda jajircewar hukumomin tsaro.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel