Jerin yan takara 11 dake gwagwarmayan neman kujerar mataimakin majalissar dattijai dana wakilai

Jerin yan takara 11 dake gwagwarmayan neman kujerar mataimakin majalissar dattijai dana wakilai

Jaridar daily trust ta bayyana cewa akalla 11 daga cikin sabbun zababbun yan majalisa sun nuna sha’awarsu akan kujerar maitamakin majalissar dattijai da wakilai a zaben majalisar dokokin na tara da zai gudana a watan Yuni.

Yayinda sabbin zababbun sanatoci shida ne suke gwagwarmaya akan kujerar mataimakin shugaban majalissar dattijai, sabbin zababbun yan majalissar wakilai biyar kuma na neman kujerar mataimakin wakilai.

Kujerar mataimakin majalissar dattijai itace ta biyu a matsayi kamar yadda mataimakin majalissar wakilai yake kusa da shugabansa.

Duk lokacin da akace shugaban majalissar dattijai dana wakilai basa nan, mataimakan su ne suke daukar aikinsu.

Wani bincike daga jaridar daily trust ta nuna cewa wai’nda suke neman kujerar mataimakin majalissar dattijai sune

Francis Alimekhena (APC, Edo),

Ovie Omo-Agege (APC, Delta),

Oluremi Tinubu (APC, Lagos),

Kabiru Gaya (APC, Kano),

Orji Uzor Kalu (APC, Abia) da

Ike Ekweremadu (PDP, Enugu).

KU KARANTA: Dalilin da yasa muka ce Ahmad Lawan ne zabin mu - Sanatocin jihar Katsina

Masu kuma neman kujerar mataimakin majalissar wakilai sun hada da

Abdulrahman Kawu Sumaila (APC, Kano),

Aminu Suleiman (APC, Kano),

Garba Muhammad Datti (APC, Kaduna),

Magaji Da’u Aliyu (APC, Jigawa) da

Abubakar Lado Suleja (APC, Niger)

Wakilin mu ya rahoto cewa daya daga cikin masu neman kujerar mataimakin majalissar dattijai da hudu dake gwagwarmaya akan kujerar mataimakin majalissar wakilai duk sun zo ne daga arewa ta yamma.

Har ila yau, Yan takara biyu masu neman kujerar mataimakin majalissar dattijai, wato Alimekhena da Omo-Agege, sun zo ne daga kudu, Sannan biyu daga ciki kuma sun zo ne daga kudu maso gabas wato yankin Igbo.

Masu neman kujerar mataimakin majalissar dattijai da wakilai, wato Oluremi Tinubu da Lado, sun zo ne daga kudu ta yamma da arewa ta tsakiya a takaice.

Duka yan takaran yan jam’iyyar APC ne amma banda Ekweremadu.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa duka yan takaran sun dau kudurin boye ma junansu niyyarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel