Mun tsare Najeriya daga Boko Haram – Ministan labarai

Mun tsare Najeriya daga Boko Haram – Ministan labarai

Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed yace gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi kokari sosai wajen magance matsalar rashin tsaro sannan ta tsare kasar fiye da yadda take a 2015.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa Mohammed ya bayyana hakan ne a Washington D.C. lokacin wata hira da muryar Amurka.

Musamman, yace gwamnatin ta yi nasarar kare gaba daya kasar daga hannun yan ta’addan Boko Haram yayinda aka kawo karshen rikicin makiyaya da manoma a Benue.

Mohammed ya bayyana cewa an sassaita yaki da ta’addanci, kashe-kashe da kuma fashi da makami a Zamfara da Kaduna cikin makonni biyu da suka gabata saboda jajircewar hukumomin tsaro.

Mun tsare Najeriya daga Boko Haram – Ministan labarai

Mun tsare Najeriya daga Boko Haram – Ministan labarai
Source: Facebook

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin za ta dauki mataki na daban baya ga tura hukumomin tsaro.

KU KARANTA KUMA: APC ta bankado wani kulli da ake yi na cinna wa ofishin INEC wuta

Yace gwamnatin na sane da abubuwan da ke haddasa rikici a yankunan da abun ya shafa ciki harda dalali na tattalin arziki, rashin kayayyakin more rayuwa da kuma ayyukan yi.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da karfafa adin gwiwa a matakan gida da na kasashen waje don magance kalubalen.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel