Orji Kalu ne zabin mu a kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa - Kabilar Ibo

Orji Kalu ne zabin mu a kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa - Kabilar Ibo

Wata kungiyar kabilar Ibo ta Ogene Igbo, ta bayyana tsohon gwamnan jihar Abia kuma zababben Sanata, Orji Uzor Kalu, a matsayin zabin ta domin ya kasance mataimakin shugaban majalisar dattawa da za a rantsar a watan Yuni.

A yayin da kungiyar ke ikirarin ba bu wanda ya cancanci kujerar face tsohon gwamnan jihar Abia Orji Kalu, ta yi kira na neman goyon bayan shugabanci da kuma sauran 'ya'ya na jam'iyyar APC da su tabbatar da wannan kudiri.

Orji Kalu tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari

Orji Kalu tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Cikin wata sanarwa ta ranar Litinin a garin Abuja, shugaban hadin kan kungiyar, Charles Mbalisi, ya nemi Kalu da ya gaggauta bayyana manufa domin samun goyon baya na jam'iyyar sa da kuma jiga-jigan ta.

Kungiyar Ogene bayan yin amanna da yadda jam'iyyar APC ta kebe shugabancin majalisar dattawa ga shiyyar Arewa maso Gabas, ta yi kira da babbar murya na neman a kebe kujerar mataimakin shugaban majalisar zuwa ga shiyyar Kudu maso Gabas domin tabbatar da adalci.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, jam'iyyar APC mai mulki tare da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, na ci gaba da muradin Sanata Ahmed Lawan na jihar Yobe ya kasance jagoran sabuwar majalisar dattawa.

KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Anambra ta tattare mabarata da mahaukata daga manyan hanyoyin birnin Onitsha

Sai dai akwai yiwuwar wannan muradi zai zamto alakakai ga jam'iyyar sakamakon rabuwar kai a tsakanin 'ya'yan ta, inda wasun su ke ganin ba bu adalci a hukuncin da uwar jam'iyyar ta yanke na zabin Sanata Lawan ba tare da an baje a faifai ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel