Atiku dan Najeriya ne – Inji Yakasai

Atiku dan Najeriya ne – Inji Yakasai

Wani jigon kasar, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar dan Najeriya ne, kuma ya cancanci takarar kowani mukami na shugabanci a kasar, ciki harda ofishin Shugaban kasa.

Yakasai, na mayar da martani ne ga wani korafi da jam’iyyar All Progressive Congress (APC) ta shigar a kotun zabe, inda tayi zargin cewa Atiku dan kasar Kamaru ne don haka, bai isa takarar Shugaban kasar Najeriya ba a zaben 2019.

Tsohon mamban kungiyar amintattu na jam’iyyar All People’s Party (APP) a wani jawabi dauke da sa hannunsa zuwa ga manema labarai a Kano, ya caccaki APC kan wannan korafi da tayi na cewa tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ba dan Najeriya bane.

Atiku dan Najeriya ne – Inji Yakasai

Atiku dan Najeriya ne – Inji Yakasai
Source: Facebook

A nawa ra’ayin, “abun al’ajabi ne ace shugabannin jam’iyya mai mulki a Najeriya, APC tayi ikirarin cewa tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar bai cancanci neman kujerar Shugaban kasa ba.

“Wannan ya nuna jahilci karara na matsayin Atiku kamar yadda yake a kundin tsarin mulkinmu. Bai kamata ace wannan furuci na fitowa daga bakin APC ba ma a cikin jam’iyyun siyasa.

KU KARANTA KUMA: APC ta bankado wani kulli da ake yi na cinna wa ofishin INEC wuta

“Akwai mutanen da jam’iyyar ta fito dasu suka yi takara har suka ci sannan kuma a yau suna rike da irin wadannan mukaman. Atiku na daidai dasu koma ace yafi su cancantar rike mukamin gwamnati a Najeriya.”

Ya kara da cewa, “Atiku dan asalin Adamawa ne wanda mahaifinsa ya kasance dan Sokoto sannan mahaifiyarsa ta kasance yar bona Fide na Adamawa sannan yan takara da dama da aka Haifa kafin shi da bayan shi ana masu kallon yan Najeriya ne."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel