APC ta bankado wani kulli da ake yi na cinna wa ofishin INEC wuta

APC ta bankado wani kulli da ake yi na cinna wa ofishin INEC wuta

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a jihar Sokoto, a ranar Litinin, 15 ga watan Afrilu ta koka kan zargin shiri da wasu mutane ke yi na cinna wa hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na jihar wuta.

Hakan na kunshe ne a wani jawabi daga sakataren labaran jam’iyyar na jihar, Sambo Bello Danchadi zuwa ga manema labarai a Sokoto.

Jawabin yace: “bayanai abun dogaro da ke iso ma shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Sokoto ya nuna cewa akwai wasu makirai da ke tattaunawa domin shirya yadda za su cinna ma hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) wuta.”

Ya kara da cewa: “Dalilin wannan ta’asar shine domin su lalata duk wasu hujojji da za a bukata a karar da aka shigar a kotun sauraron karan zaben gwamna na jihar.”

APC ta bankado wani kulli da ake yi na cinna wa ofishin INEC wuta

APC ta bankado wani kulli da ake yi na cinna wa ofishin INEC wuta
Source: Depositphotos

APC ta kara da cewa ta duba lamarin da kula sosai, inda ta bayyana cewa “hakan yunkuri ne na dakile adalci, kawo tsaiko ga damokradiyya da kuma barazana ga zaman lafiya da hadin kan jiharmu.

KU KARANTA KUMA: Majalisa ta 9: Magoya bayan Ndume sun dage akan tsarin zabe na sirri

“Don haka muna rokon dukkanin hukumomin tsaro da su lura da lamarin sannan suyi gaggawan daukar matakin da ya kamata don tabbatar da ba ofishin INEC na jihar Sokoto da takardunta kariya.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel