JAMB ta damke mutane sama hamsin dake rubutawa wasu jarabawar UTME

JAMB ta damke mutane sama hamsin dake rubutawa wasu jarabawar UTME

-Mutanen dake tafka magudi ta hanyar rubuta jarabawa ga wasu sun shiga hannu

-Sama da mutanen hamsin ne hukumar JAMB tayi nasarar damkewa a fadin kasar nan

Hukamar ta JAMB tace, ta samu nasarar damke mutum sama da hamsin wanda ke kiran kansu ‘kwararrun masu rubuta jarabawa’ wadanda suka shahara wajen rubutawa mutane jarabawa saboda a biyasu .

Fabian Benjamin, shugaban hukamar mai kula da sashen labarai ya rubuta wannan labari a shafinsu musamman na fitar da labarai mai taken ‘JAMBULLETIN’ a ranar Litinin. Manema labarai sun bayyana cewa sama da mutane miliyan daya da dubu dari takwas ne zasu rubuta wannan jarabawa ta UTME wacce aka fara tun ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu a fadin kasar nan.

Hukumar JAMB

Hukumar JAMB
Source: UGC

KU KARANTA:Buhari ya nemi goyon bayan kasashen dake makwabtaka da Najeriya wajen kare yaduwar makamai

Hukumar tace, tayi nasarar zakulo wata kungiyar dake da taken ‘kwararrun masu rubuta jarabawa’ wadanda suka shahara wurin rubuta jarabawar domin a biyasu. A sanarwar da suka fitar, bisa ga jajircewa da hukumarmu tayi ta hanyar amfani da bayanai na sirri mun samu damar cafke sama da mutane hamsin wanda ke tafka wannan ta’asa a cibiyoyin rubuta wannan jarabawar dake fadin kasar nan.

Mun sama damar fahimtar cewa, wasu daga cikin masu laifin suna da digiri na biyu wato ‘Masters’ kenan a turance inda kuma wasun su daliban jami’o’ine dake kasar nan. Zancen ya sake fayyace mana cewa su wadannan mutane sun hada kaine da masu wadannan cibiyoyi na zana jarabawar ta JAMB inda suke zuwa yayinda za’a dauki hoton yastun wanda yazo rejista domin rubuta jarabawar sai suma ayi amfani harda nasu.

“Lokacin da ake tuhumar masu laifin, jigo daga cikinsu ya shaida mana cewa suma din ana daukar hoton yatsun nasu ne tare da asalin masu zana wannan jarabawa tare da biyansu kudi masu tarin yawa.

“Wannan dalilin ne ya sanya hukumar zata sake yin wani hoton yan yatsu na masu zana jarabawar a karo na biyu domin ya basu damar damke wadanda ke shirya magudi da kuma cuta akan wannan jarabawa tare da masu basu goyon baya.

“A karshe hukamar na shirin bin hanyoyin shari’a domin a gurfanar da masu wannan laifi a gaban kotu kana kuma ayi musu hukuncin da ya dace dasu. A cewarta cigaba da aukuwar irin wannan laifin zai kawo cikas da kuma tabarbarewar gudanar da jarabawar ga baki daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel