Majalisa ta 9: Magoya bayan Ndume sun dage akan tsarin zabe na sirri

Majalisa ta 9: Magoya bayan Ndume sun dage akan tsarin zabe na sirri

- Wasu zababbun sanatocin jam’iyyar APC da ke goyon bayan Sanata Ali Ndume sun dage kan cewa lallai sai dai a gudanar da tsarin zabe na sirri wajen zabar shugabanin majalisar dokokin kasar na tara

- Sanatocin sunce cin zarafi ne ace wasu abokan aikinsu na neman tsarin zabe bayananne a zaben shugabannin majalisar

- Sun kaddamar da cewa furucin shugabancin APC na aika mumunan alamu ne ga yan majalisa kan shugabancinta

Wasu zababbun sanatocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ke goyon bayan Sanata Ali Ndume sun dage kan cewa lallai sai dai a gudanar da tsarin zabe na sirri wajen zabar shugabanin majalisar dokokin kasar na tara.

Ndume wanda ke wakiltan Borno ta kudu a majalisar dokokin kasar na daya daga cikin sanatocin APC biyu da suka ce lallai sai sun yi takarar shugabancin majalisar dattawa duk da cewar jam’iyyar ta tsayar da Sanata Ahmad Lawan.

Dayan sanatan da ke takarar shine Danjuma Goje, tsohon gwamnan jihar Gombe kuma sanata mai wakiltan Gombe ta tsakiya a majalisar dokokin kasar.

Majalisa ta 9: Magoya bayan Ndume sun dage akan tsarin zabe na sirri

Majalisa ta 9: Magoya bayan Ndume sun dage akan tsarin zabe na sirri
Source: Facebook

Sanatocin, wadanda suka yi hira da jaridar ThisDay a ranar Litinin, 15 ga watan, sunce cin zarafi ne ace wasu abokan aikinsu na neman tsarin zabe bayananne a zaben shugabannin majalisar.

KU KARANTA KUMA: Yadda na samu kudi daga hannun su Fayose inji Manajan Banki

Biyu daga cikin masu goyon bayan Ndume sun kaddamar da cewa furucin shugabancin APC na aika mumunan alamu ne ga yan majalisa kan shugabancinta.

Daya daga ciki sanatocin daga arewa maso gabas yace: “Mu na Ndume ne kuma babu wani barazana da zai sa mu sauya matsayarmu. Mu dai tsaya mu jira har sai an rantsar damu a watan Yuni.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel