An tsare wani direba kan zargin yiwa yarinya yar shekara 13 fyade

An tsare wani direba kan zargin yiwa yarinya yar shekara 13 fyade

- Wata kotun majistare da ke da zama a Ibadan ta tsarewani direban mota, Wale Oladeji, a kurkukun Agodi kan zargin lalata yarinya yar shekara 13

- Yarinyar ta kasance dalibar karamar makarantar sakandare

- Yayi wa yarinyar fyade ne a bandakin shagon mahaifiyarta a ranar 28 ga watan Maris

Mai shari’a a babbar kotun majistare na Iyaganku da ke Ibadan, a ranar Litinin, 15 ga watan Afrilu, tayi umurnin tsare wani direban mota, Wale Oladeji, a kurkukun Agodi kan zargin lalata yarinya yar shekara 13 wacce ta kasance dalibar karamar makarantar sakandare.

Hukumar yan sanda ta tuhumi Oladeji dan shekara 30, wanda ke zama a gida mai lamba 27, Itamaya Oke-Ado, Ibadan, da laifin fyade.

Mai shari’an, Misis Olabisi Ogunkanmi bata amshi rokon wanda ake kara ba.

An tsare wani direba kan zargin yiwa yarinya yar shekara 13 fyade

An tsare wani direba kan zargin yiwa yarinya yar shekara 13 fyade
Source: Depositphotos

Ogunkanmi ta bayar da umurnin, zuwa lokacin da za a ji shawara daga sashin doka na jihar Oyo.

Ta dage zaman zuwa ranar 7 ga watan Mayu, don ci gaba da shari’a.

KU KARANTA KUMA: Yadda na samu kudi daga hannun su Fayose inji Manajan Banki

Dan sanda mai kara, sufeto Sikiru Opaleye, ya fada ma kotun cewa Oladeji ya aikata laifin ne a ranar 28 ga watan Maris, da misalin karfe 4 na rana, inda yayi wa yarinyar fyade a bandakin shagon mahaifiyarta.

Mahaifiyar yarinyar ce ta kai rahoton lamarin sashin bincike na jihar, Iyaganku, Ibadan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel