Sai da na gina matatun man fetur uku a fadin kasar nan lokacin mulki na - Yakubu Gowon

Sai da na gina matatun man fetur uku a fadin kasar nan lokacin mulki na - Yakubu Gowon

A kokarin da gwamnatin tarayya ta ke yi na cire tallafin man fetur a kasar nan, tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Yakubu Gowon ya bayyana irin kokarin da gwamnatin sa ta yi wurin gina matatun man fetur uku a fadin kasar nan

A jiya ne tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Yakubu Gowon (Rtd), ya bayyana cewa gwamnatin sa ta gina matatun man fetur guda uku a fadin kasar nan, daya a jihar Kaduna, daya a Fatakwal daya kuma a Warri, sannan kuma ta na da burin gina wasu matatun man fetur din, domin fita da shi zuwa kasashen duniya , ba wai ta dinga sayarwa kasashe danyan man ba.

Hakan ya biyo bayan sanarwar da karamin ministan man fetur na kasa Dakta Ibe Kachikwu ya ce zai yi wuya gwamnatin tarayya ta iya cire tallafin man fetur a wannan lokacin don ta kare al'ummar kasa.

Sai da na gina matatun man fetur uku a fadin kasar nan lokacin mulki na - Yakubu Gowon

Sai da na gina matatun man fetur uku a fadin kasar nan lokacin mulki na - Yakubu Gowon
Source: Depositphotos

Gowon ya ce: "Ina son sanar da ku cewa a lokacin da na yi mulki na so na gina matatu guda biyar ne a kasar nan, wanda za su taimakawa kasar wurin sayar da man fetur a kasuwannin duniya.

"Matatun man fetur na Fatakwal, Warri da Kaduna, duka an yi su ne da tsarin za a dinga amfani da su a cikin gida Najeriya, sannan daga baya sai a dinga fita da man fetur din zuwa kasashen ketare."

KU KARANTA: Sai na yi nazari kafin na karbi mukami a hannun shugaba Buhari - Dan takarar shugaban kasa

A na shi bangaren Kachikwu ya ce, gwamnatin tarayya ta na duba yiwuwar cire tallafin man fetur din, idan har zai yi amfani ga rayuwar al'umma.

Ya ce: "Duk wani shugaban kasa da zai yi amfani da wannan shawarar ya kamata ya tsaya ya yi tunanin abinda zai je ya dawo."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel