PDP ta bukaci shugaba Buhari ya tanadi takardun sa na Sakandare don kare kanshi a kotu

PDP ta bukaci shugaba Buhari ya tanadi takardun sa na Sakandare don kare kanshi a kotu

- Bayan sanarwar da Festus Keyamo ya fitar na cewa ba dole sai mutum na da takardun sakandare zai yi mulki a Najeriya ba mutukar ya na iya magana da harshen turanci

- Yanzu haka dai jam'iyyar PDP ta kara tabbatar da cewar shugaba Buhari ba shi da takardun sakandare, inda ta bukaci ya tanade su domin kare kanshi a kotu

Babbar jam'iyyar adawa PDP ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tanadi takardunsa na makarantar sakandare, don kare kanshi a kotu.

Jam'iyyar ta bayyana hakan bayan sanarwar da mai magana yawun shugaban kasar Festus Keyamo ya fitar a gidan talabijin na Channel, inda ya ke nuna cewa ba dole sai mutum ya na da takardun sakandare zai yi shugaban kasa ko gwamna a Najeriya ba.

PDP ta bukaci shugaba Buhari ya tanadi takardun sa na Sakandare don kare kanshi a kotu

PDP ta bukaci shugaba Buhari ya tanadi takardun sa na Sakandare don kare kanshi a kotu
Source: UGC

A wata sanarwa wacce mai mai magana da yawun jam'iyyar PDP ya fitar, Kola Ologbondiyan, jam'iyyar ta bukaci 'yan Najeriya da su lura da magaanar da Keyamo yayi na cewar ba dole sai mutum ya na da takardun sakandare ba zai iya mulki a Najeriya mutukar zai iya magana da harshen turanci, hakan ya na nuni da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba shi da takardun makarantar sakandare.

KU KARANTA: Hukumomin tsaro sun binciko wata makarkashiya da Atiku ya ke hadawa Buhari

Kola ya kara da cewa, abinda shugaban kasar ya yi bai kyauta ba tunda har ya rantse a kotu akan cewar yana da takardun sakandare bayan kuma ba haka maganar ta ke ba.

PDP ta cekokarin yaudarar al'umma ta yin amfani da takardun bogi ba zai taimakawa shugaban kasar ba.

Bayan haka kuma sashe na 295 na kundin tsarin mulkin kasa na 1999, ya na da cikakken bayani akan hukuncin wanda ya yi amfani da takardun bogi.

Jam'iyyar PDP ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tabbatar da ya tanadi takardun sa domin kare kanshi a kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel