Dakatar da Onnoghen na da nasaba da siyasa

Dakatar da Onnoghen na da nasaba da siyasa

- Timi Frank yace akwai lauje cikin nadi kan al'amarin Onnoghen

- Hadimar Buhari ta bayyana daya daga cikin dalilan da yasa aka takawa Onnoghen birki

Tsohon mataimakin sakataren sadarwa na jam’iyar APC, Timi Frank yayi suka akan dakatar da Onnoghen lamarin da ya danganta shi da furucin hadimar Buhari wato Lauretta Onochie, inda ya bayyana cewa zaton da wasu keyi akan dakatar da Onnoghen akwai siyasa a ciki nada kamshin gaskiya.

A ranar Lahadi ne Onochie tayi ikirarin cewa Onnoghen yayi shirin kawo cikas a zaben ranar 23 ga watan Febrairu na shugaban kasa a jihohi goma sha bakwai ta hanyar soke zabukan kana kuma ya baiwa dan jami’iyar PDP wato Atiku Abubakar nasara.

Onnoghen, Buhari

Onnoghen, Buhari
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Babu batun janye tallafin man fetur a yanzu, inji Ministar Kudi

Wannan maganar ke nuna cewa dakatarwar ba wai ta tsakani da Allah ce aka yiwa Onnoghen ba a cewar Frank. Ya kara da cewa “wannan zancen tamkar kara tabbatarwa ne bisa ga abinda muka riga muka sani.”

Bugu da kari, ya ce “Wannan abu ai tamkar cin zarafine ga mutumin da bai aikata laifin komi ba wanda gwamnatin Buhari tayi domin a sauya kudurin jama’ar kasar. Har wa yau, Frank ya sake cewa dama can fadar shugaban kasa bata da niyar gudunar da sahihin zabe."

Haka zalika, “Da yan Najeiya zasu tuna, wanda fa ya fara kawo korafin a dakatar da Onnoghen, mai suna Denis Agbanya ya kasance tsohon hadimi ne na Buhari kuma har yanzu yana daya daga cikin mutanensa na kusa. Kuma korafin ma an gabatar dashi ne a gaban kotu ranar 12 ga watan Janairu, 2019 wacce rana ce da kowa ya san kotu bata zama cikinta.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel