Shugaba Buhari zai karbi bakuncin zababbun yan majalissar wakilai yau

Shugaba Buhari zai karbi bakuncin zababbun yan majalissar wakilai yau

Jaridar daily trust ta bada rahoton cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bakunci zababbun yan majalissar wakilai a fadar Aso Villa dake birnin Abuja a yau Talata, 16 ga watan Afrilu, 2019.

Taron zai gudana ne bayan kwana 21 da karbar bakuncin zababbun sanatoci yan jamiyyar APC a fadar.

Wata majiya ta bayyana cewa taron zai gudana ne tare da shugaban jamiyyar APC wato Adams Oshiomhole da kuma wasu yan kwamitin gudanarwan jam'iyyar.

Duk da cewan ya bayyana karara cewa jam'iiyar APC dan majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, take so, Ana kyautata zaton cewa jamiyyar za ta bayyana dan takararta na kujerar kakakin majalissa.

KU KARANTA: Jiragen ruwa 18 sun shigo Nigeria da ton 357,396 na man fetir

A bangare guda, Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai fara sabuwar gwamnatin shi da wani salo na sallamar duka ministoci amma zai bar daya ko biyu daga cikinsu, Majiya daga fadar shugaban kasa ya bayyana hakan.

Sabanin abinda ya faru a 2015 da ya dauke shi tsawon watanni shida kafin ya bayyana ministocin shi,wannan karan zai bayyana su a watan Yunin 2019.

Jaridar THIS DAY ta bayyana cewa shugaba Buhari yana takatsantsan akan zaben ministocin sa ne wanda zasu taimaka mai wajen wanzar da alkawuran da ya yiwa yan Nigeria.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel