Dalilin da yasa muka ce Ahmad Lawan ne zabin mu - Sanatocin jihar Katsina

Dalilin da yasa muka ce Ahmad Lawan ne zabin mu - Sanatocin jihar Katsina

Dukkan sanatocin jihar Katsina uku sun alanta cewa sun yanke shawaran marawa takarar Sanata Ahmad Lawan baya a matsayin shugaban majalisar dattawan Najeriya bisa ga dalilin cewa shine mafi cancanta cikin wadanda ke takarar kujeran.

Sanata Bello Mandiya mai wakiltar Katsina Kudu ya yi jawabi madadin sanatocin yankin inda yace bisa ga kwarewan da Ahmad Lawan ya samu na tsawon shekaru 20 a majalisar dattawa, ya zama dole a zabeshi saboda babu wanda ya kaishi dadewa a majalisar.

Yace: "A yanzu haka, matsayin (Lawan) na shugaban masu rinjaye kadai zai bashi nasara. A kasashen duniyan masu cigaban demokradiyya, ko zabe ba za'ayi ba, itifaki kawai za'a yi."

"Hakan ya faru ba da dadewa ba a Amurka. Mun amince dashi kuma muna girmamashi. Musamman kasancewan Lawan ba zai yaudari shugaban kasa kuma jagoranmu shugaba Muhammadu Buhari ba."

KU KARANTA: Sojoji sun yiwa gari a Zurmi zobe, sun hallaka yan bindiga da dama, sun damke wasu

Sauran Sanatocin biyu sune Kabir Barkiya mai wakiltar Kastina ta tsakiya, da Ahmad Baba-Kaita mai wakiltar Katsina na Arewa.

A wani labarin mai kama da haka, Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya bayyana cewa al'ummar Borno za ta samu nasara kan Sanata Ali Ndume domin ya janyewa Sanata Ahmad Lawan, wanda jam'iyyar APC ta zaba matsayin dan takaranta na kujerar shugaban majalisar dattawa.

Shettima ya bayyana cewa a matsayinsu na masu biyayya ga jam'iyya, ya kamata su amince da zabin jam'iyyar kan ahmad Lawan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel