Najeriya na fitar da gangan mai miliyan 2.019 a duk rana ta Allah – Inji NNPC

Najeriya na fitar da gangan mai miliyan 2.019 a duk rana ta Allah – Inji NNPC

Hukumar man fetir ta Najeriya, NNPC, ta sanar da cewa a duk rana Najeriya na fitar da gangan danyen mai guda miliyan biyu da dubu goma sha tara, (2,019,000), kamar yadda shugaban NNPC, Maikanti Baru ya bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Baru ya bayyana haka ne a yayin taron kasa da kasa akan harkar tama karo na sha biyu daya gudana a babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, 15 ga watan Afrilu, inda ya bayyana wasu daga cikin cigaban da aka samu a NNPC.

KU KARANTA: Abu naku maganin a kwabeku: Gwamna ya ware naira miliyan 13 don kiran waya

Baru yace tun bayan darewarsa shugabancin NNPC, an samu cigaba a adadin danyen man da ake fitarwa a Najeriya daga miliyan 1.86 a shekarar 2017 zuwa 2.019 a shekarar 2018, wanda hakan ke nuna samun karuwa da kashi 9.

Shugaban ya kara da cewa an samu yawaitan man fetir a Najeriya a yan shekarun nan fiye da shekarun baya, inda yace a shekarar 2018 sun sayar da man fetir lita biliyan 1.2, ba kamar shekarar 2017 da aka sayar da litan biliyan 1.1 ba.

Haka zalika Maikanti Baru ya bayyana ma mahalarta taron cewa NNPC a karkashin shugabancinsa ta samu gagarumar nasara a kokarin da take yin a hakarman fetir a wurare da dama a fadin kasar, musamman ma a tafkin Kolmani, inda yace sun haka fiye da zurfin kafa dubu goma.

A wani laabrin kuma, an fara samun dogayen layukan motoci a gidajen mai a jahohin Kano da Kaduna, yayin da wasu gidajen man suka dakatar da sayar da mai, wanda hakan yasa jama'a suka shiga fargaban ko za'a fara wahalar mai ne, amma dai NNPC tace akwai isashshen mai a kasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel