Rashin Mai: Jiragen ruwa 18 sun shigo Nigeria da ton 357,396 na man fetir

Rashin Mai: Jiragen ruwa 18 sun shigo Nigeria da ton 357,396 na man fetir

Yayinda Najeriya ke cigaba da fama da rashin isasshen man fetur a wasu jihohin kasar, har da jihar Legas da Abuja, bincike ya nuna cewa akalla jiragen ruwa goma za su dira tashohoshin ruwa daban-daban karshen wannan mako.

Ana da tabbacin cewa jirage guda takwas din da suka riga suka shigo a baya sun gama juye man fetir din a karshen makon.

Jimaillan Jirage 18 din na dauke da ton 357,396 na man fetir wanda zasu kai Jihar lagos.

Bisa wata sanarwa da hukumar jiragen ruwa ta kasa tayi, tace daya daga cikin jiragen ruwa mai suna St James zai bada 38,000MT na fetir a ranar litinin 15 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai bakunci zababbun yan majalissar wakilai yau

Jiragen ruwan da zasu jibge a tashan Atlas Cove sune: Nord Sustainable dauke da ton 37,562, BW Marlin dauke da ton 38,000, High Sea dauke da ton 37,986, MT Hafina Atlantic dauke da ton 37,951 da MT Lacerta dauke da ton 37,868.

A bangare guda, Gwamnatin tarayya ta sake bayyana kudurinta dangane da janyen tallafin man fetur inda tace ba ta da niyyar yin hakan a nan kusa.

Ministar kudi, Zainab Ahmed ce tayi wannan furuci a ranar Lahadi yayinda take tsokaci akan taron da ya gudana na hadaka tsakanin Kungiyar kudi ta duniya wato ‘IMF’ da kuma Bankin duniya a babban birnin Amurka, Washington DC.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel