Abu naku maganin a kwabeku: Gwamna ya ware naira miliyan 13 don kiran waya

Abu naku maganin a kwabeku: Gwamna ya ware naira miliyan 13 don kiran waya

A yayin da talaka ku kukan babu kudi a kasa, kudi yayi karanci a tsakanin jama’a, su kuwa shuwagabannin Najeriya ko a jikinsu, sakamakon suna kula da baitul malin gwamnati, don haka suke facaka da kudi son ransu.

Anan gwamnatin jahar Ondo ce ta ware ma ofishin gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu naira miliyan goma sha uku (N13,000,000) don sanya katin kiran waya a kasafin kudin shekarar 2019, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Farawa da iyawa: Kotu ta sallami wani sabon dan majalisar APC tun ba’a rantsar da shi ba

Abu naku maganin a kwabeku: Gwamna ya ware naira miliyan 13 don kiran waya

Gwamna Akeredolu
Source: Depositphotos

Haka zalika an kasafta kudi naira miliyan dari biyar (N500,000,000) don tarbar manya baki da ake sa ran zasu halarci wasu muhimman bukukuwa ko taruka da gwamnatin jahar zata dauki nauyi a cikin shekarar 2019.

Sai dai shima mataimakin gwamnan ba’a barshi a baya ba, inda aka ware naira miliyan biyar don sa katin waya a ofishinsa, sai kuma naira miliyan biyu da aka kasafta don sa katin a waya a ofisoshin manyan hadiman gwamnan.

Bugu da kari gwamnatin ta kasafta naira miliyan dari uku da talatin da shida don sayan kayan tsaraba da kyaututtuka da zata rabar a yayin bukukuwan kananan yara da kuma naira miliyan dari biyu da talatin don sallama, shima ofishin mataimakin gwamna an ware msa naira miliyan hamsin don bayar da kyauta.

Wannan wadaka bai tsaya nan ba, inda aka kasafta wasu kudaden don amfanin ofishin gwamna, inda aka ware naira miliyan dari da bakwai don tafiye tafiyen cikin gida, naira miliyan biyu kudin wutar lantarki, da kuma miliyan 25 don sayen kayan aiki a Ofis da kwamfutoci.

Duk a cikin wannan kasafin kudi na bana wanda tuni majalisar dokokin jahar ta amince dashi, an ware miliyan 53 don gyaran motoci, miliyan 150 don ciye ciye da shaye shaye da dai sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel