Watakila yau a amince da kasafin kudin Najeriya na bana

Watakila yau a amince da kasafin kudin Najeriya na bana

Bisa dukkan alamu ‘yan majalisar dattawa da na wakilai na iya kammala aikin kasafin kudin Najeriya na shekarar nan ta 2019 a yau dinnan kamar yadda mu ke samun labarai daga jaridun kasar nan.

Rahotanni sun nuna cewa ana iya amincewa da kasafin kudin na bana a yau dinnan Laraba, 16 ga Watan Afrilun 2019. Alamu sun nuna cewa kwamitocin da ke kula da harkar kasafin kudi a majalisar dattawa da wakilai sun bazama aiki.

Labaran da mu ke samu shi ne ‘yan majalisar kasar za su gabatar da rahoton aikin kasafin na bana a rana guda ne domin gudun samun tangardar da za ta sa a dakatar da amincewa da kundin kasafin na wannan shekarar a majalisar.

Tun tuni dai shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, yayi alkawarin cewa a rana irin ta yau ne za su karkare duk wani aiki da ya shafi kasafin kasar. Saraki ya ba wannan kwamiti wa’adi ne har zuwa Ranar Talata watau 9 ga Watan Afrilu.

KU KARANTA: Babban Sanatan APC zai tsere ya koma PDP bayan ya ci zabe

Watakila yau a amince da kasafin kudin Najeriya na bana

A yau Majalisa tayi alkawarin karasa aikin kasafin kudin 2019
Source: Depositphotos

Shugaban majalisar tarayyar na kasar ya gargadi kwamitin kasafin da yayi maza ya kammala duk aikin da ke gaban sa ko kuma a tilastawa majalisar aiki da lissafin da aka kawo mata cikin kundin kasafin ba tare da an canza wani abu ba.

A cikin farkon makon jiya, an koka da cewa kwamitin kasafin na majalisar dattawa wanda Sanata Mohammed Danjuma Goje yake jagoranta bai karasa aikin sa ba, inda aka ji cewa kwamitoci 24 ne cikin 61 su ka iya karasa aikin su.

Majiyar mu ta bayyana mana cewa a halin yanzu, Sanata Danjuma Goje da kwamitinsa, sun kusa kammala duk aikin da ake bukata, kuma abin da ya rage kurum shi ne a gabatar da wannan aiki a gaban majalisu 2 na kasar a zaman yau.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel