Omo Agege zai sauya-sheka zuwa PDP bayan ya rusa APC– O’tega Emehor

Omo Agege zai sauya-sheka zuwa PDP bayan ya rusa APC– O’tega Emehor

Mun samu labari kwanan nan cewa wani babban jagoran jam’iyyar APC a jihar Delta, O’tega Emerhor, ya zargi Sanatan APC na jihar watau Ovie Omo-Agege da kashe jam’iyyar ta APC a jihar Delta a zaben 2019.

O’tega Emerhor, yake cewa Sanata Ovie Omo-Agege mai wakiltar Delta ta tsakiya a majalisar dattawa ya kawowa APC matsala a zaben 2019. A cewar Emerhor, Omo Agege ya zo APC ne tun farko domin ya kashe jam’iyyar ba komai ba.

A wani jawabi da Mista O’tega Emerhor ya fitar a Ranar Litinin dinnan 15 ga Watan Afrilun 2019, Jigon na APC ya zargi fitaccen Sanatan kasar da fara shirye-shiryen komawa babbar jam’iyyar adawar Najeriya PDP kwanan nan.

KU KARANTA: Omo Agege: An maka majalisar Dattawan Najeriya a gaban kotu

Babban ‘Dan siyasar yace Sanatan zai tattara kayan sa yanzu ya koma PDP inda daga nan ya fito tun can, bayan ganin ya jefa APC ta jihar Delta cikin halin da ta shiga a zaben 2019. Emerhor yace tun can dama Agege ‘Dan adawar APC ne.

Emerhor ya bayyana yadda ‘dan majalisar yayi amfani da jam’iyyar sa ta Labor Party wajen yi wa shugaba Buhari da kuma APC adawa a zaben 2019. Daga baya ne dai ya sauya-sheka ya kuma kafa yaran sa a cikin tafiyar ta APC a jihar Delta.

Sai dai irin su O’tega Emerhor su na ganin cewa Omo Agege da mutanen sa da su ka shigo APC daga baya sun kawo hatsaniya a jam’iyyar. A dalilin haka ne dai aka samu bangaren ‘Yan Taware na Ogoboru/Agege a cikin tafiyar APC

KU KARANTA: Abubuwa 10 da ya kamata ka sani game da Sanata Ovie Omo-Agege

Emerhor ya kuma ce shi ne ya budewa Omo-Agege kofar dawowa APC a 2017 amma yanzu yace ‘dan majalisar ya zama tamkar cutar kansa a APC ta jihar Delta. Emerhor yace asali, Omo Agege ne sanadiyyar rashin da APC tayi a Delta.

Yanzu dai ana ta faman rikici a kotu inda bangaren Cif Great Ogboru su ke ikirarin cewa su ne ke da takarar gwamna. Emerhor yace Omo-Agege ya fara harin takarar gwamna ne a PDP a 2023 don haka yake tunanin barin jam’iyyar APC.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel