Farawa da iyawa: Kotu ta sallami wani sabon dan majalisar APC tun ba’a rantsar da shi ba

Farawa da iyawa: Kotu ta sallami wani sabon dan majalisar APC tun ba’a rantsar da shi ba

Wata kotun daukaka kara dake zamanta a garin Bini na jahar Edo ta soke takarar wani zababben dan majalisar wakilai daya tsaya takara a karkashin inuwar tsintsiyar jam’iyyar APC, Peter Akpatason.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Akpatason ya lashe zaben dan majalisa mai wakiltar al’ummar mazabar Akoko-Edo ne a zabukan da suka gabata na watan Feburairu, sai dai shari’a sabanin hankali, kotu kuma tayi masa tutsu.

KU KARANTA: Kallabi tsakanin rawwuna: Yadda wata Ustaziya tayi zarra a tsakanin daliban ABU

Haka zalika kotun ta bayyana rashin ingancin matakin da kwamitin sauraren korafe korafen zaben fidda gwani na jam’iyyar APC ta dauka, dake karkashin jagorancin tsohon gwamnan jahar Edo, Farfesa Osunbo Oserheimen, na bayyana Akpatason a matsayin sahihin dan takarar APC.

Alkalin kotu, mai sharia Moore Abraham-Adumein ya bayyana cewa kaakakin majalisar dokokin jahar Edo, Kabiru Adjoto ne halastaccen dan takarar jam’iyyar APC a mazabar Akoko-Edo, don haka Alkalin ya caccaki babbar kotun da ta fara sauraron karar bisa rashin yin aikinta yadda ya kamata.

Alkali Moore ya kara da cewa hatta kwamitin sauraron korafe korafen zabukan fidda gwani na APC bashi ba halastacce bane sakamakon ya saba ma sashi na 21b na kundin dokokin jam’iyyar APC kanta, sa’annan ya tabbatar Kabiru ya lashe zaben fidda gwani da kuri’u 7,034, yayin da Akpatason ya samu 5,606.

Daga karshe Alkalin ya tabbatar da Kabiru Adjoto a matsayin halastacce kuma zababben sabon dan majalisa da zai wakilci mazabar Akoko-Edo a majalisar wakilai ta tara, sa’annan ya umarci korarren dan majalisa Akapatason ya biyashi diyyar N300,000 kudaden daya kashe wajen neman hakkinsa.

Sai dai lauyan Akpatason, Omoh-Ige Adebayo ya bayyana cewa basu gamsu da wannan hukuncin ba, don haka zasu daukaka kara zuwa kotun Allah-Ya-isa, watau kotun koli kenan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel