Babban Kotu ta nemi a garkame Ibrahim Wala a gidan kurkuku

Babban Kotu ta nemi a garkame Ibrahim Wala a gidan kurkuku

Babban kotun tarayya da ke zama a Abuja ta daure fitaccen ‘dan gwagwarmayar nan watau, Ibrahim Wala wanda aka fi sani da IG Wala. Kotu tace ta samu wannan Bawan Allah da aikata laifuffuka.

Alkali mai shari’a Yusuf Halilu na kotun tarayya da ke Unguwar Maitama ya bayyana cewa kotu ta samu IG Wala da laifin aikata laifuffuka 3 cikin laifuffuka 4 da shugaban ‘yan sandan Najeriya da Ministan shari’a su ke zargin sa da su.

Kotu tace ta samu IG Wala da laifin tara jama’a ba tare da bin ka’ida ba, sannan kuma ta same sa da laifin tinzira mutane da kuma jifar wani da laifi. Kotu har wa yau tayi watsi da daya daga cikin laifin da ake tuhumar wannan Bawan Allah.

An maka Ibrahim Wala a kotu ne bayan da shugaban hukumar NAHCON da ke kula da aikin Hajji a Najeriya, Abdullahi Mukhtar, ya kai karar cewa shi IG Wala yana kokarin ci masa zarafi da kuma bata masa da hukumar NAHCON suna.

KU KARANTA: Abin da ya sa na na shiga harkar satar mutane mu na garkuwa

Wala ya zargi shugaban wannan hukuma ta NAHCON da yin sama da fadi da wasu kudi har Naira Biliyan 3 a aikin hajjin da aka yi a 2017, sai dai Alkali mai shari’a yace IG Wala ya gaza tabbatar da wannan zargi da yake yi wa Mukhtar.

Kotu ta kuma bayyana cewa kungiyar CATBAN da IG Wala ya kafa ba ta da rajista a Najeriya, wanda shi kan sa hakan laifi ne. Yunkurin tunzura mutane a kan shugaban hukumar Mahajjatan shi kan sa ya sabawa dokar final kwad inji Kotu.

Mista Ibrahim Wala ya saba fita zanga-zanga inda yake gwagwarmaya domin karbowa Bayin Allah hakkin su a Najeriya. IG Wala ya kuma saba kokawa da irin zaluncin da ake yi wa marasa karfi a kasar nan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel