Fyade budurwa: Kotu ta aika aminan juna; Ali da Sadiq, zuwa gidan yari

Fyade budurwa: Kotu ta aika aminan juna; Ali da Sadiq, zuwa gidan yari

Wata kotun majistare da ke garin Ilorin a jihar Kwara ta bayar da umarnin tsare wasu abokai biyu a gidan yari bisa zarginsu da hada baki tare da aikata fyade ga wata budurwa mai shekaru 19.

Majistare Monisola Kamson ta bayar da umarnin a tsare Sadiq Abdulrauf da Ali Ahmad a gidan yari na Oke-kura, a garin Ilorin.

Ta daga sauraron karar zuwa ranar 2 ga watan Mayu.

Dan sanda mai gabatar da kara, saja Gbenga Ayeni, ya shaida wa kotu cewar matasan sun yiwa budurwar fyade bayan ta rako wata kawarta gidan wani abokinsu.

Yeni ya ce masu laifin tare wani abokinsu, Korani, wanda ya tsere, sun yiwa budurwar duka kafin daga bisani su yi mata fyade.

Fyade budurwa: Kotu ta aika aminan juna; Ali da Sadiq, zuwa gidan yari

Fyade budurwa: Kotu ta aika aminan juna; Ali da Sadiq, zuwa gidan yari
Source: Twitter

Sai dai, bayan an karanta musu tuhumar da ke kansu, sun ce basu aikata hakan ba.

Mai gabatar da karar ya ce laifin da wadanda ake tuhumar suka aikata ya saba da sashe na 97 da na 282 na kudin fenal kod.

DUBA WANNAN: Zamfara: Buhari zai kaddamar da sabbin jiragen yaki na musamman

Ya nemi alfarmar kotu da ta tsare wadanda ake tuhuma a gidan yari har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel