Zamfara: Buhari zai kaddamar da sabbin jiragen yaki na musamman

Zamfara: Buhari zai kaddamar da sabbin jiragen yaki na musamman

Shugaban rundunar sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar, ya ce nan bada dadewa ba shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da wasu jiragen yaki na musamman guda biyu domin kara bunkasa yaki da 'yan bindiga a yankin arewa maso yamma.

Sadique ya bayar da wannan tabbaci ne yayin hutun karshen mako a wurin bikin bude wasu sabbin gine-ginen wurin kwana da aka yi a hedikwatar sojin sama da ke Maiduguri, jihar Borno.

Ya bukaci dakarun soji da su kara tsananta wa a atisayen da suke yi domin yaki da 'yan bindiga da aiyukan ta'addanci a yankuna arewa maso yamma da arewa maso gabas.

Zamfara: Buhari zai kaddamar da sabbin jiragen yaki na musamman

Air Marshal Sadique Abubakar
Source: Depositphotos

"Ina mai kira ga dakarun rundunar sojin sama, maza da mata, da su cigaba da yin aiki tukuru wajen bayar da gudunmawarsu a atisayen tabbatar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas da arewa maso yamma; za mu cigaba da yin aiku tukuru domin ganin dukkan 'yan Najeriya sun samu zaman lafiya da zai basu damar gudanar da harkokinsu na kasuwanci cikin kwanciyar hankali.

DUBA WANNAN: Wasu tsageru sun kashe dan sanda a ofishin INEC a Bakassi

"Mu na sa ran samun karin kayan aiki, a takaice, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da wasu jiragen yaki masu saukar ungulu da ke dauke da bindigu domin yakar 'yan ta'adda a yankin arewa maso yamma, ta yadda manoma zasu samu sukunin yin noman damuna a gonakinsu ba tare da fargabar za a kashe su ba," a cewar sa.

Shugaban rundunar sojin saman ya ce ya gamsu da irin nasarar da ake samu daga atisayen da dakarun soji da sauran jami'an tsaro ke gudanarwa domin tsarkake Najeriya daga gurbatar da tayi da 'yan ta'adda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel