Wasu tsageru sun kashe dan sanda a ofishin INEC a Bakassi

Wasu tsageru sun kashe dan sanda a ofishin INEC a Bakassi

Rundunar 'yan sanda a jihar Kuros Riba ta tabbatar da mutuwar wani jami'inta mai mukamin kwansatabul da wasu tsageru suka kashe a ofishin hukumar zabe ta kasa (INEC) da ke karamar hukumar Bakassi.

Da ta ke tabbatar da kisan jami'in, DSP Irene Ugbo, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ya ce an kashe dan sandan ne yayin da ya ke bakin aikinsa.

Wasu tsageru ne suka kawo farmaki ofishin na INEC tare da kashe jami'in dan sandan da ke aiki a wurin, kamar yadda Irene ta fada.

Tayi watsi da zargin cewar kisan na da alaka da zabukan shekarar 2019 da aka kammala. "A'a, ko kadan kisan dan sandan bashi da wata alaka da INEC," kamar yadda ta fada.

Ta bayyana cewar tuni rundunar 'yan sanda ta fara binciken kisan jami'in da aka yi ranar Litinin. Sai dai rundunar 'yan sandan ba ta bayyana sunan jami'in da aka kashe ba.

Wasu tsageru sun kashe dan sanda a ofishin INEC a Bakassi

Wasu tsageru sun kashe dan sanda a ofishin INEC a Bakassi
Source: Depositphotos

Wasu shiadar gani da ido sun bayyana wa manema labarai a garin Calabar cewar dan sandan ya mutu ne sakamakon rashin samun taimakon gaggawa yayin da jini ke zuba daga jikinsa sakamakon harbin da aka yi masa.

DUBA WANNAN: Kachikwu, ministan man fetur ya bayyana dalilin wahalar man fetur a wasu jihohi

Wani bincike da aka gudanar a tsakanin mazauna Bakassi ya nuna cewar har yanzu tsagerun yankin na cigaba da cin karensu babu babbaka, duk da yafiyar da gwamnatin jiha da ta tarayya tayi masu bayan sun fito sun shaida tare da nuna wa duniya cewar sun ajiye makamansu.

Tsagerun yankin Bakassi na tsula tsiyarsu ne karkashin wata kungiya 'Bakassi Strike Force' da wani mai suna Benjamin Ene, wanda aka fi kira da 'Janar Franklyn, ke jagoranta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel