Kachikwu, ministan man fetur ya bayyana dalilin wahalar man fetur a wasu jihohi

Kachikwu, ministan man fetur ya bayyana dalilin wahalar man fetur a wasu jihohi

- Tun a cikin makon jiya aka fara yada jit-jitar cewar gwamnatin tarayya za ta cire tallafin man fetur kacokan

- An fara yada jita-jitar ne biyo bayan shawarar da kungiyar lamunin kudi ta duniya (IMF) ta bawa Najeriya a kan ta cire tallafin man fetur

- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewar babu shirin cire tallafin man fetur din a halin yanzu

Karamin ministan albarkatun man fetur, Dakta Ibe Kachikwu, ya ce an samu dogayen layuka a gidajen man fetur da ke wasu jihohin kasar nan ne sakamakon gibin da aka samu a jigilar mai, ya ce dogayen layukan ba su da alaka da karancin man fetur.

Da ya ke magana da 'yan jarida a Legas, Kachikwu ya bukaci jama'a da su yi watsi da jita-jitar cewar za a yi karin farashin man fetur.

Ministan ya yi wannan jawabi ga manema labaran ne a wurin bude wani taro na kasa da kasa a kan man fetur da iskar gas, wanda aka yi a Legas.

Kachikwu, ministan man fetur ya bayyana dalilin wahalar man fetur a wasu jihohi

Dakta Ibe Kachikwu, ministan man fetur
Source: Depositphotos

Ya ce babu wani lokaci da jagororin gwamnati suka zauna, suka yi magana a kan karin farashin man fetur da jama'a ke cigaba da yada wa.

"Na samu damar kewaya wa wasu gidajen man fetur kuma na gani da idona yadda dogayen layika suka ragu a gidajen man. Batun karin farashin man fetur wata magana ce da ke bukatar duba na tsanaki.

DUBA WANNAN: Ana shan bakar wuya a mulkin Buhari - Jarumar fim

"Gwamnati za ta mu'amalanci 'yan kasuwar man fetur kafin ta zartar da kowanne hukunci.

"Akwai damuwa a kan yadda dogayen layi suka dawo gidajen man fetur duk da irin tabbacin da NNPC ta bayar," a cewar Kachikwu.

Ya bayyana kwarin gwuiwarsa a kan NNPC da jagororinta, ya na mai bayyana cewar tuni aka warware matsalar da aka samu wajen jigilar man fetur da ta haddasa dawowar dogayen layuka a gidajen mai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel