Gwamnatin jihar Anambra ta tattare mabarata da mahaukata daga manyan hanyoyin birnin Onitsha

Gwamnatin jihar Anambra ta tattare mabarata da mahaukata daga manyan hanyoyin birnin Onitsha

Da sanadin jaridar Vanguard mun samu rahoton cewa, gwamnan jihar Anambra Cif Willie Obiano, ya fadada akidar sa kyautatawa wajen gudanar da ayyukan jin kai ga masu yawon barace-barace da kuma masu cutar tabin hankali a jihar sa.

Ga masu bibiyar labarai, a shekarar da ta gabata ga gwamnatin jihar Anambra ta aiwatar da makamancin wannan lamari na tattare mabarata da masu cutar tabin hankali masu kwashe dare a cikin kwatami da gefen hanyoyi na jihar.

Gwamnan jihar Anambra; Willie Obiano

Gwamnan jihar Anambra; Willie Obiano
Source: Depositphotos

A wannan lokacin gwamnatin jihar da sanadin ma'aikatar jin dadin zamantakewa, Mata da kuma kananan Yara, ta shiga cikin birnin Onitsha inda ta tattare masu yawon barace-barace da masu tabin hankali da ke sintiri da kai komo a manyan hanyoyi.

Rahotanni kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito sun bayyana cewa, mafi akasarin mabaratan sun kasance Mata da kuma kananan Yara da ke cin karen ba bu babbaka da sunan sana'a ta bara.

Ko shakka ba bu gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Obiano ta aiwatar da wannan gagarumin aiki domin tsarkake jihar daga masu yawon barace-barace da kuma masu cuta ta tabuwar hankali daga manyan hanyoyin ta.

KARANTA KUMA: 'Yan ta'adda sun yi garkuwa da Mutane 5, sun bukaci fansar N10m a jihar Kogi

Kazalika jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, gwamnati ta jibge mabarantan da masu tabuwar hankali da ta tattare a cibiyar kulawa ta Nteje Rehabilation Centre domin duban lafiyar su tare da ba su mangunguna gami da wayar masu da kai.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel