El-Rufa'i ya nada sabon kwamishinan kudi da babban akawun jihar Kaduna

El-Rufa'i ya nada sabon kwamishinan kudi da babban akawun jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya nada Alhaji Bashir Saidu a matsayin sabon kwamishinan ma'aikatar kudi ta jihar Kaduna.

Saidu, shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Kaduna, zai maye gurbin Suleiman Kwari, mutumin da aka zaba a matsayin sanata a zaben da aka kammala.

A jawabin da mai taimaka wa gwamna El-Rufa'i a bangaren yada labarai, Samuel Aruwan, ya fitar a Kaduna, ya ce aikin da ke gaban sabon kwamishinan shine "kawo canje-canje masu amfani da muhimmanci a ma'aikatar kudi da za su taimaka wa gwamnatin Nasir El-Rufa'i wajen warware irin kalubalen da zata iya fuskanta a zango na biyu."

Kazalika, jawabin ya bayyana cewar an nada Mista Idris Samaila Nyam a matsayin sabon babban akawun jihar Kaduna, yayin da aka nada Umar Waziri, tsohon babban akawun jihar, a matsayin sabon babban manajan kamfanin harkokin saka hannun jari da kudi na jihar Kaduna.

El-Rufa'i ya nada sabon kwamishinan kudi da babban akawun jihar Kaduna

Nasir El-Rufa'i
Source: UGC

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar Nyam, kafin nadinsa a matsayin babban akawu, ya kasance babban sakatare a ma'aikatar kudi, mukamin da ake sa ran daya daga cikin manyan darektoci a ma'aikatar zai maye gurbin.

DUBA WANNAN: Kotun daukaka kara ta mayar wa da Ibrahim Baba na APC kujerar sa a Filato

Sanarwar ta kara da cewa Dakta Salisu Suleiman, babban sakataren gwamna, zai cigaba da gudanar da harkokin ofishin shugaban ma'aikatan gidan gwamnati.

Dukkan sabbin nade-naden za su fara aiki nan take, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel