'Yan ta'adda sun yi garkuwa da Mutane 5, sun bukaci fansar N10m a jihar Kogi

'Yan ta'adda sun yi garkuwa da Mutane 5, sun bukaci fansar N10m a jihar Kogi

Wani mashahurin direban motar haya mai sunan Sapamo, ya afka tarkon masu garkuwa da mutane tare da fasinjoji hudu a kan hanyar su ta Ayetoro/Gbede dake yankin Ijumu zuwa garin Kaaba na jihar Kogi.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, masu garkuwa da mutane sun dawo da cin kasuwar su a babbar hanyar Obajana bayan da hukumomin tsaro su ka tsarkake hanyar daga duk wani nau'i na ta'addanci.

'Yan ta'adda sun yi garkuwa da Mutane 5, sun bukaci fansar N10m a jihar Kogi

'Yan ta'adda sun yi garkuwa da Mutane 5, sun bukaci fansar N10m a jihar Kogi
Source: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa, Sapamo tare da fasinjojin sa hudu sun afka tarkon masu garkuwa da mutane a kan hanyar su ta dawowa daga birnin Lokoja inda ba tare da aune ba azal ta afka masu da tsakar ranar Litinin.

Daya daga cikin makusanta Sapamo da masu garkuwa da mutane suka tuntuba ta hanyar wayar tarho, ya ce sun nemi fansa ta Naira Miliyan 10. Sai dai yayin neman rangwami sun sassauta farashi inda suka amince da biyan N4m ga dukkanin Mutane biyar da suka yi garkuwa da su.

KARANTA KUMA: Neman abinci ya sanya na shiga ta'addancin garkuwa da satar shanu - 'Dan ta'adda

A yayin tattara wannan rahoto, manema labarai sun gaza samun dama ta ganawa da kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Kogi, Williams Anya, sakamakon rashin amsa kiran wayar sa ta salula.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel