Kotun daukaka kara ta mayar wa da Ibrahim Baba na APC kujerar sa a Filato

Kotun daukaka kara ta mayar wa da Ibrahim Baba na APC kujerar sa a Filato

Kotun daukaka kara, reshen jihar Filato, da ke zamanta a Jos ta mayar wa da Ibrahim Baba Hassan, mamba mai wakilatar mazabar Jos North/North a majalisar dokokin jihar Filato, kujerarsa bayan wata babbar kotu da ke zamanta a Jos ta kwace kujerar daga hannunsa bisa zargin cogen takardun karatu.

Tun a shekarar 2015 ne Abdul Nasir Saleh ya shigar da karar dan majalisar a kan zargin cewar ya gabatar da takardar shaidar kammala karatun difloma a kan harkokin kasuwanci daga jami'ar Jos ta bogi.

Saleh ya zo na biyu a zaben fidda 'yan takara da jam'iyyar APC ta gudanar a jihar Filato a shekarar 2014.

Kotun ta cire dan majalisar, sannan ta umarce shi ya biya wanda ya yi kararsa diyyar N25m tare da mayar da dukkan kudin albashi da alawus-alawus da ya karba zuwa aljihun gwamnati.

Sai dai bayan kotun ta yanke hukuncin karbe kujerar daga hannun dan majalisar, lauyansa, Solomon Umoh, ya daga kara zuwa kotun daukaka kara, reshen Jos.

Kotun daukaka kara ta mayar wa da Ibrahim Baba na APC kujerar sa a Filato

Kotun daukaka kara ta mayar wa da Ibrahim Baba na APC kujerar sa a Filato
Source: Twitter

A sabon hukuncin hadin gwuiwa da alkalan kotun; Mudassiru Oneyangi, Tani Hassan da Habeeb Abiru, suka yanke, sun jingine hukuncin da kotun farko ta yanke bisa hujjar cewa mai kara ya shigar da korafi bayan shudewar kwanaki 14 da kammala zabukan cikin gida da jam'iyyar APC ta gudanar a shekarar 2014.

DUBA WANNAN: Kin biyan haraji: Kotun Najeriya ta bayar da umarnin kama Okocha

Jastis Oneyangi ya ce kotun ta shafe fiye da shekaru uku tana sauraron karar, tare da bayyana cewar sashe na 285 (10) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 19999, ya yi bayanin cewar kar babbar kotu ta haura kwanaki 180 kafin ta yanke hukunci a kan korafe-korafen kafin zabe.

Amma lauyan da ke kare mai kara, David Ibeawuchi, ya ce za su nazarci hukuncin kafin daukan mataki na gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel