Kin biyan haraji: Kotun Najeriya ta bayar da umarnin kama Okocha

Kin biyan haraji: Kotun Najeriya ta bayar da umarnin kama Okocha

Wata babbar kotun jihar Legas da ke zamanta a Igbosere ta bayar da sabon umarnin a kama tsohon kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Najeriya (Super Eagles), Augustine Okocha, bisa kin biyarn haraji.

Alkalin kotun ya bayar da sabon umarnin ne bayan babban mai gurfanar da jama'a a jihar Legas, Mista Yusuf Sule, ya roki kotun ta kara sabunta hukuncin da ta fara yanke wa a kan Okocha tun ranar 29 ga watan Janairu.

Sule ya shaida wa kotun cewar Okocha ya ki cika alkawarin sulhunta wa da hukuma, kamar yadda aka yi yarjejeniya a baya, a kan tuhumarsa da laifin kin biyan haraji a shekarar 2017.

Kazalika, ya ce Okocha ya ki bayyana a kotun tun bayan zuwansa na farko a ranar 5 ga watan Oktoba na shekarar 2017.

Kin biyan haraji: Kotun Najeriya ta bayar da umarnin kama Okocha
Austin Okocha
Asali: Depositphotos

Sai dai, Okocha bai halarci kotun ba kuma babu wani lauya da ke kare shi da ya halarci zaman kotun.

Sule ya kara da cewa Okocha ya tuntubi hukumar tattara haraji ta jihar Legas (LIRS) amma har yanzu bai biya ko sisi ba.

"Wanda ake karar ya nuna niyyar biyan kudin, amma har yanzu bai bayar da ko sisi ba

"A saboda haka ne muke son kotu ta kara sabunta hukuncinta na farko," a cewar Sule.

DUBA WANNAN: Tuna baya: Abubuwan da Sa'adu Zungur ya fada a kan makomar arewa shekaru 61 da suka wuce

Da ya ke amince wa da bukatar Sule, alkalain kotun, Akintoye, ya ce: "umarnin neman a kamo wanda ake kara yana nan daram.

"An daga sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Mayu."

An fara shigar da karar Okocha ne a ranar 6 ga watan Yuni na shekarar 2017, bisa zarginsa da aikta laifuka masu nasaba kauce wa biyan haraji ga gwamnatin jihar Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel