Rayuka 15 sun salwanta, Mutane 14 sun jikkata a harin jihar Nasarawa

Rayuka 15 sun salwanta, Mutane 14 sun jikkata a harin jihar Nasarawa

Mun samu rahoton cewa, rayukan Mutane 15 sun salwanta yayin da Mutane 14 su ka jikkata a harin daren jiya Lahadi da ya auku cikin kauyen Numa da ke garin Andaha na karamar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa.

Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan bindiga dadi sun zartar da ta'addanci kan al'ummar kauyen Numa yayin da su ke tsaka da gudanar da shagulgula na dare.

Rayuka 15 sun salwanta, Mutane 14 sun jikkata a harin jihar Nasarawa

Rayuka 15 sun salwanta, Mutane 14 sun jikkata a harin jihar Nasarawa
Source: UGC

Cikin nasa jawaban, shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah reshen jihar Nasarawa, Alhaji Muhammad Hussaini, cikin yakini ya ce maharan ba su da nasaba ta kusa ko ta nesa da Fulani illa iyaka miyagun ababe ne masu kishi da zaman lafiya.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Alhaji Hussani ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta gudanar da bincike domin cafke wadanda su ka aikata wannan mummunar ta'ada ta fasadi a ban kasa.

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda na jihar, DCP Umwar Shehu Nadada, yayin tabbatar a aukuwar lamari ya ce Fulani ba su da hannu cikin wannan ta'addanci illa iyaka 'yan bindiga dadi da ba bu wata masaniya a kansu.

KARANTA KUMA: ASUU ta kalubalanci tanadin da gwamnatin tarayya ta yiwa ilimi a kasafin kudin kasa na bana

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, mahara rike da bindigu sun salwantar da rayukan Mutane 15 tare da raunata Mutane 24 cikin yankin Gwandara na karamar hukumar Jema'a ta jihar Kaduna.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel